Kishiyar Dangote, BUA Zai Bude Sabon Kamfanin Sarrafa Siminti Bayan Karya Farashi

Kishiyar Dangote, BUA Zai Bude Sabon Kamfanin Sarrafa Siminti Bayan Karya Farashi

  • Kamfanin simini na BUA ya shirya tsaf domin kaddamar da babban kamfanin sarrafa siminti a Sokoto
  • Shugaban rukunin kamfanonin BUA, Abdul Samad Rabiu, ya bayyana wannan ci gaban a wata ziyara da ya kai wa gwamnan jihar Sokoto
  • Ya ce rukunin kamfanonin BUA shi ne mafi girma wajen samar da ayyukan yi a Arewa maso Yamma na kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Sokoto - Daya daga cikin manyan masu sarrafa siminti a Nigeria, kamfanin BUA, mallakin Abdul Samad Rabiu, ya bayyana shirin da yake yi na bude sabon kamfanin sarrafa siminti a jihar Sokoto a watan Janairu, 2023.

Rabiu, shugaban rukunin kamfanonin BUA, ya bayyana hakan a wata ziyara da ya kai wa gwamnan jihar Sokoto Ahmad Aliyu a ranar Laraba, Legit ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shugaban NLC ya shiga yanayi, za a fitar da shi zuwa kasar waje neman lafiya

Abdul Samad Rabiu BUA
BUA ya ce kamfanin sa ne mafi girma wajen samar da ayyukan yi a Arewa maso Yamma Hoto: Bloomberg / Hoton kamfanin siminti domin bayani kawai
Asali: Getty Images

Shugaban kasa Bola Tinubu shi ne bako na musamman a ranar

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hamshakin dan kasuwar ya ce kamfanin BUA, wanda a baya-bayan nan ya karya farashin simintinsa a Nigeria, na aiki tukuru domin ganin ya kammala duk wasu shirye shirye na fara aikin kamfanin kafin ranar kaddamar da shi.

Rabiu ya kuma shaida wa gwamnan cewa ya sanar da shugaban kasa Bola Tinubu batu kan kaddamar da sabon kamfanin, a wata ziyara da ya kaiwa shugaban kasar a ranar Talata, 31 ga watan Oktoba, 2023, kamar yadda jaridar BusinessDay ta ruwaito.

Ya ce ya gayyaci shugaban kasar a matsayin babban bako a ranar kaddamarwar, yana mai jaddada cewa kamfanin simintin BUA a jihar shi ne mafi girma wajen samar da ayyukan yi a shiryyar Arewa maso Yamma.

Kara karanta wannan

Shugaban NLC ya magantu kan yadda aka lakada masa duka a jihar Imo

Kamfanin simintin BUA ya samu karancin riba a shekarar 2023

Abdul samad ya kuma taya gwamnan jihar murnar samun nasara a zabensa, tare da yin alkawarin bayar da duk wata gudunmawa domin gudanar da nasarar ayyukan gwamnatin Aliyu.

Gwamna Aliyu a nasa jawabin, ya jinjina wa rukunin kamfanonin BUA bisa gudunmawar da suke bayarwa na ayyukan ci gaba a jihar.

A hannu daya kuma, rahotanni sun nuna cewa kamfanin ya bayyana cewa ya samu ribar N85.75b a ranar Talata, 31 ga watan Oktoba, 2023, a cikin watanni tara.

Sai dai wannan ribar ta yi kasa da kaso 3.4 idan aka kwatanta ta da ribar N88.81 da kamfanin ya samu a shekarar 2022, kamar yadda ThisDay ta ruwaito.

Kamfanin Simintin BUA Ya Karya Farashin Siminti Zuwa N3,500 Kan Kowani Buhu

Kamfanin simintin BUA, wanda shine kamfanin siminti mafi girma na biyu a kasuwar Najeriya, ya sanar da rage farashin buhun siminti zuwa N3,500, Legit Hausa ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tinubu zai kashe Naira Biliyan 1.5 wajen sayo motocin uwargidar Shugaban kasa

A cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X a ranar Lahadi, 1 ga watan Oktoba, kamfanin ya ce sabon farashin zai fara tasiri daga ranar Litinin, 2 ga watan Oktoba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.