Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da CoS Na Shugaban Majalisar Dokokin Adamawa, Sun Turo Sako
- Yan bindiga sun yi garkuwa da shugaban ma'aikatan kakakin majalisar dokokin jihar Adamawa, Usman Sahabi
- Rahotannin da aka tattara sun nuna cewa maharan sun kai masa farmaki har gida da daddare, suka tafi da shi zuwa cikin daji
- Rundunar ƴan sanda ta ce jami'anta sun bazama suna aiki ba dare ba rana domin tabbatar da ya kuɓuta cikin ƙoshin lafiya
Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa da al'amuran yau da kullum
Jihar Adamawa - Tsagerun ƴan bindiga sun yi awon gaba da Usman Sahabi, shugaban ma'aikatan kakakin majalisar dokokin jihar Adamawa (CoS), Bathiya Wesley.
Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, ƴan ta'addan sun sace Sahabi ne daga gidansa da ke garin Wurro-Chekke a ƙaramar hukumar Yola ta Kudu a jihar Adamawa.
Majiyoyi daban-daban sun bayyana cewa maharan ɗauke da muggan makamai sun farmaki gidan ɗan jaridan da misalin ƙarfe 1:00 na tsakar dare wayewar garin Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ɗaya daga cikin majiyoyin masu ƙarfi ta ce:
"Su biyar ne ƴan bindigan da suka kutsa kai cikin gidansa da ƙarfe 1:00 na safiyar yau ɗin nan Alhamis, suka fasa ɗakinsa suka shiga, suka tasa shi zuwa maɓoyar su."
Sahabi, ma’aikacin gidan radiyon Adamawa (ABC), ya ɗaukar rahoto daga majalisar kafin shugaban majalisar ya nada shi shugaban ma’aikatansa.
Shin sun nemi kuɗin fansa?
Wani ɗan uwan Sahabi ya shaida wa jaridar cewa masu garkuwan sun tuntubu dangi, kuma har sun nemi Naira miliyan 20 a matsayin kuɗin fansar Sahabi.
Yayin da take tabbatar da faruwar lamarin, rundunar ƴan sanda reshen jihar Adamawa ta lashi takobin ceto ɗan jaridar cikin ƙoshin lafiya.
Ba zamu runtsa ba - Yan sanda
Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar, SP Sulaiman Nguroje, ya ce tuni aka tura dakaru da sauran kayan aiki don tabbatar da ceto sahabi daga hannun masu garkuwa.
A rahoton Daily Post, kakakin ƴan sandan ya ce:
“Mun tura jami'anmu tare da kayan aiki kuma muna aiki ba dare ba rana don ganin an ceto dan jaridar da aka sace da ransa."
Bam ya halaka mutane a Yobe
A wani rahoton da Legit Hausa ta kawo muku mayaƙan Boko Haram sun dasa wa masu zuwa jana'iza bam a jihar Yobe kuma aƙalla mutane 20 suka mutu nan take.
Rahotanni sun nuna cewa mutanen sun dawo daga makokin matasa 17 da aka kashe a yankin ƙaramar hukumar Gaidam ranar Litinin.
Asali: Legit.ng