Rusau: Kotu Ta Umarci Gwamnatin Abba Ta Biya ‘Yan Kasuwa N30bn Nan da Kwanaki 7

Rusau: Kotu Ta Umarci Gwamnatin Abba Ta Biya ‘Yan Kasuwa N30bn Nan da Kwanaki 7

  • Za a fara dabbaka hukuncin da kotun tarayya ta zartar a shari’ar masu shago a masallacin idi da gwamnatin jihar Kano
  • Alkali ya ce wajibi ne gwamnatin Kano ta fara ajiye kudin a asusun kotu kafin a kammala daukaka karar da aka yi
  • Samuel Amobeda ya ce kin yi wa kotunsa biyayya na nufin gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta na wasa da hankalin shari’a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Kano - Babban kotun tarayya mai zama a Kano ta umarci gwamnatin jihar ta biya diyyar Naira biliyan 30 nan da kwanaki bakwai masu zuwa.

Leadership ta ce hakan ya biyo bayan wata kara da shugabannin kungiyar masu shaguna a masallacin idin birnin Kano su ka kai gwamnatin jiha.

Lauyoyin da su ka shigar da kara sun nemi dabbaka hukuncin da aka zartar a Satumba, ana umartar gwamnati ta biya ‘yan kasuwan N30bn.

Kara karanta wannan

Naira Biliyan 7.5 da Tinubu zai kashe a gyaran gida a Legas ya fusata ‘yan Najeriya

Gwamnan Kano
Gwamnan Kano zai biya 'yan kasuwa N30bn Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Abba zai fitar da N30bn a kwana 7

Alkali Samuel Amobeda wanda ya saurari karar ya ce dole ne a ajiye kudin a cikin asusun bankin kotun, za ayi wannan ne nan da mako guda.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukuncin ya na nufin gwamnatin Abba Kabir Yusuf za ta biya kudin kafin a kai karshen shari’ar, gwamnatin NNPP ta daukaka karar a kotu.

Kwamishinan ayyuka na jihar Kano, Injiniya Marwan Ahmed zai fuskanci fushin kotu idan ya cigaba da sabawa wannan hukunci da kotu ta yi.

Kano: Sabawa hukunci zai iya jawo dauri

Jaridar Tribune ta ce Mai shari’a Samuel Amobeda ya yi barazanar cewa kotu za ta iya daure wanda aka samu da laifi muddin ba ayi biyayya ba.

Ganin nasarar da 'yan kasuwan su ka fara samu, Alkali ya ce za a za a iya samun bayanan asusun bankin daga mataimakin magatakardar kotu.

Kara karanta wannan

Kano: Kujerar Majalisar Tarayya da kotu ta karbe ya dawo hannun NNPP a karshe

Babban lauyan gwamnati kuma Kwamishinan shari’a na Kano ya ce Gwamnati ta mallaki shagunan saboda haka babu dalilin biyan diyya.

Rusau: Abba Gida Gida a Kano

Gwamna Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida bai wuce kwanaki uku da hawa mulki ba aka ji ya fara rusa wasu gine-gine.

A sakamakon shari’ar mai lamba FHC/KN/Cs/208/2023 da aka yi, aikin sabon Gwamnan ya jawowa jihar Kano asarar makudan biliyoyi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel