Dakarun Sojoji Sun Ceto Mutum 4 da Ƴan Bindiga Suka Sace a Kebbi
- Dakarun sojojin Najeriya tare da haɗin gwiwar ƴan sakai sun samu nasarar ceto mutum huɗu da ƴan bindiga suka sace a Kebbi
- Dakarun sojojin sun samu wannan nasarar ne a wani sumame da suka kai maɓoyar ƴan bindigan a tsaunin Bangi na jihar
- Tawagar sojojin da ƴan sakan sun kuma samu nasarar fattakar ƴan bindiga masu yawa a cigaba da ƙoƙarin magance matsalar tsaro a jihar
Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi
Jihar Kebbi - Dakarun sojojin Najeriya tare da ƴan sakai sun samu nasarar ceto wasu mutum huɗu da ƴan bindiga suka yi garkuwa da su a tsaunin Bangi da ke a ƙaramar hukumar Suru ta jihar Kebbi.
Sojojin da suka fito daga bataliya ta 1, ta rundunar sojojin Najeriya, a Birnin Kebbi, sun kuma fatattaki ƴan ta'adda da dama a yaƙin da suke yi da masu tayar da ƙayar baya, cewar rahoton Tribune.
Daraktan tsaro na ofishin majalisar zartarwar jihar Kebbi, Abdulrahman Usman ne ya bayyana haka ga manema labarai a Birnin Kebbi a daren ranar Laraba, 1 ga watan Nuwamban 2023, rahoton Daily Post ya tabbatar
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A kalamansa:
"Da misalin ƙarfe 4:00 na rana na ranar 1 ga watan Nuwamban 2023, dakarun sojoji na bataliya ta 1, Birinin Kebbi tare da haɗin gwiwar ƴan sakai sun gudanar da sintiri na yaƙi zuwa tsaunin Bangi dake ƙaramar hukumar Suru."
"A yayin farmakin, rundunar ta kori adadi mai yawa na ƴan bindiga da kuma ceto mutum huɗu da aka yi garkuwa da su."
Ya bayyana cewa mutanen huɗu da aka ceto sune, Malam Audu Fulani mai shekara 45, Umaru Wakili mai shekara 14, Alhaji Imam mai shekara 50 da kuma Chaggo Garba mai shekara 19.
Ana samun cigaba wajen murƙushe ƴan bindiga
Usman ya tabbatar da cewa jami'an tsaro na samun nasara kan ƴan ta'adda a jihar tun daga lokacin da Gwamna Nasir Idris Kauran Gwandu ya ba su umarnin murƙushe su da ƙarin kayan aiki.
Ya kuma yabawa gwamnan bisa goyon bayan da yake baiwa jami’an tsaro bisa kokarin da suke yi na kawo ƙarshen matsalolin tsaro a jihar.
Dakarun Sojoji Sun Ceto Mutum 24
A wani labarin kuma, dakarun sojoji a jihar Zamfara sun samu nasarar ceto mutum 24 da ƴan bindiga suka sace.
Dakarun sojojin sun ceto mutanen ne a ƙaramar hukumar Maru ta jihar a wani sumame da suka kai kan maɓoyar ƴan bindigan.
Asali: Legit.ng