Shin Tinubu Bai Nemi a Siya Ma Sa Jirgin Ruwa Na Alfarma? Kakakin Shugaban Ya Yi Bayani
- Shugaba Tinubu ya karyata jita-jitar cewa ya ware makudan kudade don siyan jirgin ruwan alfarma a fadarsa
- Kakakin Shugaba Tinubu, Tope Ajayi shi ya bayyana haka a yau Alhamis 2 ga watan Nuwamba a Abuja
- Wannan na zuwa ne bayan an yada cewa Tinubu ya ware wasu kudade daga cikin karin kasafi don siyan jirgin ruwan
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja – Shugaba Bola Tinubu ya musanta cewa ya nemi a siya ma sa jirgin ruwa na alfarma.
Kakakin shugaban, Tope Ajayi shi ya bayyana haka a yau Alhamis 2 ga watan Nuwamba a Abuja, Legit ta tattaro.
Wane cece-kuce ake yi kan jirgin ruwan Tinubu?
An yi ta cece-kuce cewa Shugaba Tinubu ya mika karin naira tiriliyan 2.1 na kasafin kudi ga majalisar Tarayya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga cikin kasafin, naira biliyan 5.9 an ware su ne don siyan jirgin ruwa na alfarma don shugaban yayin da aka ware naira biliyan 2.9 don wata mota na alfarma a fadar.
Har ila yau, naira biliyan 2.9 an ware su ne don sauya tsoffin motoci da ke fadar shugaban kasar da su ka ji jiki.
Mene ya jawo cece-kuce kan jirgin ruwan Tinubu?
Daily Trust ta tattaro cewa jirgin ruwan da ake magana a kai na daga cikin kasafin Hukumar Sojin Ruwa na naira biliyan 42.3.
Yayin da ya ke martani, Ajayi ya ce ya na mamakin yadda Tinubu zai bukaci wannan jirgin ruwan don yin amfani da shi a ofishinsa.
Hausa Legit ta ji ta bakin wasu kan wannan lamari:
Muhammad Aliyu ya ce ko mutum duka duniyar ya siya watarana ai zai barta, ya kamata a yi wani abu a kan haka.
Sale Muhammad ya ce:
"Idan a Najeriya ka ke babu abin da wallahi ba za ka gani ba, sai kace mun fi kowa shugabanni a duniya."
Tinubu zai kashe biliyan 5 kan gyaran tsohon gida
Kun ji cewa, Shugaba Tinubu ya ware naira biliyan biyar don gyaran tsohon gidansa da ke Legas.
Wannan na zuwa ne yayin da ake zargin shugaban ya ware naira biliyan 5 don siyan jirgin ruwa.
Asali: Legit.ng