'Yan Ta'adda Sun Tare Babbar Hanya a Zamfara, Sun Kashe Mutane da Dama Tare da Sace Wasu Masu Yawa
- Miyagun ƴan ta'adda sun tare babban titin hanyar Funtua-Gusau da tsakar rana a ranar Laraba, 1 ga watan Nuwamba
- Ƴan ta'addan sun halaka mutane masu yawa tare da yin awon gaba da wasu mutanen da ba a san adadinsu ba a yayin harin
- Daga cikin waɗanda harin ya ritsa da su har da tsohon ɗan majalisar wakilai a jihar Zamfara wanda shi kaɗai ne aka kai asibiti da ransa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wakilin Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar fiye da shekara biyar wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi
Zamfara: Ƴan ta'adda sun kashe wasu mutane da ba a san adadinsu ba, da yin garkuwa da wasu da dama a yammacin ranar Laraba, a lokacin da suka kai wa wasu motoci hari a kan babban titin hanyar Funtua-Gusau a jihar Zamfara.
Jaridar Premium Times ta ce an kuma jikkata wasu mutane da dama a harin. Ɗaya daga cikin wadanda suka jikkata shi ne tsohon ɗan majalisar wakilai na Mafara/Anka a jihar Zamfara, Kabiru Yahaya.
Yadda ƴan ta'addan suka kai mummunan harin
Mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Musbahu Aliyu, ya ce maharan sun tare babbar hanyar ne a tsakanin Kucheri-Magazu a ƙaramar hukumar Tsafe da misalin ƙarfe 3:30 na rana.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Ƴan ta'addan sun jira isowar ababen hawan take amfani da hanyar inda suka fara harbi ba kakkautawa wanda hakan ya sa aka toshe hanyar." A cewarsa.
Ya bayyana cewa tsohon ɗan majalisar ne kaɗai aka kai babban asibitin Tsafe da ransa.
"Babu wanda ya san adadin waɗanda aka kashe ko aka sace. Sun yi awon gaba da dukkanin fasinjojin da ke cikin motar farko." A cewar Aliyu.
Ya ƙara da cewa an mayar da ɗan siyasar zuwa wani asibiti da ke babban birnin jihar, Gusau.
Wani majiya mai suna Murtala ya ce harin ya auku ne ƴan mintuna kaɗan bayan ya wuce wurin.
Ya ce ya ji ƙarar harbe-harbe mintuna kaɗan kafin ya isa Tsafe. Ya ce ya ga motocin sojoji da dama sun garzaya zuwa wurin da aka kai harin.
Ƴan ta'adda na yawan kai hare-hare a Zamfara
Harin na ranar Laraba ya auku ne kwanaki kaɗan bayan da ƴan ta'adda suka kai hari a wani shingen binciken ƴan sanda da ke da tazara kaɗan daga garin Tsafe, inda suka halaka ƴan sanda uku a harin.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Yazid Abubakar, bai amsa kiran da aka yi masa ta waya ko dawo da saƙon da aka tura masa ba domin jin ta bakinsa game da harin.
Ƴan Bindiga Sun Sace Mutane a Kaduna
A wani labarin kuma, wasu miyagun ƴan bindiga sun halaka wani mutum ɗaya tare da sace wasu mutum 25 a jihar Kaduna.
Ƴan bindigan sun kai harin ne a Ungwan Baka a gundumar Agunu cikin ƙaramar hukumar Kachia da ke Kudancin jihar.
Asali: Legit.ng