Naira Biliyan 7.5 da Tinubu Zai Kashe a Gyaran Gidan Legas Ya Fusata ‘Yan Najeriya

Naira Biliyan 7.5 da Tinubu Zai Kashe a Gyaran Gidan Legas Ya Fusata ‘Yan Najeriya

  • Bola Ahmed Tinubu ya bukaci majalisar tarayya ta amince masa kashe karin Naira tiriliyan 2.17 kafin karshen shekarar nan
  • Biliyoyin kudi za su tafi a wajen gyaran gidajen shugaban Najeriya da mataimakinsa da sayen manyan-manyan motoci
  • Ganin abubuwan da ke kunshe cikin kasafin kudin ya batawa mutane rai, a daidai lokacin da ake fama da tsadar rayuwa a kasa

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Mai girma Bola Ahmed Tinubu, ya ware Naira biliyan 4 domin gyaran tsohon gidan shugaban kasa da ke barikin Dodan a garin Legas.

Kamar yadda Legit ta samu bayani daga kwarya-kwaryar kasafin kudin 2023, gwamnatin tarayya za ta batar da kudin nan a gyare-gyare.

Kara karanta wannan

Bayan naira triliyan 2.17, majalisar dattawa ta lamuncewa Tinubu ciyo bashin $7.8Bn da €100M

Bola Tinubu
Mai girma Shugaba Bola Tinubu Hoto: @Dolusegun
Asali: Twitter

Tinubu zai kashe Biliyoyi a kan gyaan gida

Abin bai tsaya nan ba, rahotanni sun tabbatar da cewa za a kashe kusan Naira biliyan 2 domin gyaran gidan mataimakin shugaban kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gidajen su na tsohon fadar shugaban kasa da aka zauna a Legas kafin a dawo Abuja.

Abin bai tsaya a nan ba, Premium Times ta ce gwamnati ta bukaci a amince mata kashe Naira biliyan 4 domin gina wasu ofisoshi a Aso Rock.

Bola Tinubu ya kuma kudiri niyyar kashe Naira biliyan 3 da sunan gyaran rukunin gidajen hukumar EFCC da su ke Mabushi da Guzape a Abuja.

Kasafin kudi ko facakar kudi?

Ana zargin gwamnati da kasafta abubuwan da ba su da matukar muhimmanci a lokacin da ya dace a tsuke bakin aljihu saboda karancin kudi.

Masu sharhi a kan al’amuran yau da kullum sun ce shugabanni ba su cika amfani da fadar da ke Legas ba tun da Abuja ta koma birnin tarayya.

Kara karanta wannan

Tinubu zai kashe Naira Biliyan 1.5 wajen sayo motocin uwargidar Shugaban kasa

Rahoton ya ce bai fi sau hudu Muhammadu Buhari ya ziyarci gidan shugaban kasa da ke Legas ba, sai dai Bola Tinubu tsohon gwamnan jihar ne.

Daily Trust ta ce motoci kurum da za a tanada domin fadar shugaban kasa za su lakume fiye da Naira biliyan 6 a yayin da ake tsadar fetur.

Tinubu zai sayo kwale-kwale na sama da Naira biliyan 5, zamantar da na’urorin fadar shugaban kasa da ake so ayi zai cinye Naira miliyan 200.

Bola Tinubu zai saye motocin uwargida

Rahoto ya tabbatar da cewa kudin motocin Remi Tinubu da na Shugaban kasa da za a saya za su isa a sayen buhunan shinkafa 800, 000 a kasuwa.

Sabon kasafin kudin da aka aikawa majalisar tarayya cike ya ke da abubuwan da ‘yan Najeriya da-dama su ke ganin ba a bukatarsu a yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel