Jami’an EFCC Sun Kama Daliban OAU 70 Yayin Wani Samamen Cikin Dare, Sun Yi Martani

Jami’an EFCC Sun Kama Daliban OAU 70 Yayin Wani Samamen Cikin Dare, Sun Yi Martani

  • Hukumar EFCC a jihar Osun ta kai farmaki dakunan kwanan dalibai a Jami’ar Obafemi Awolowo da ke jihar
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa hukumar ta kama akalla dalibai 72 tare da kwace wayoyinsu da motoci
  • Sai dai har zuwa wannan lokaci hukumar ba ta yi bayani kan musabbabin kamun daliban ba da ake ta cece-kuce

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Osun – Hukumar Yaki da Cin Hanci (EFCC) ta cafke daliban Jami’ar Obafemi Awolowo 70 a daren jiya Talata a jihar Osun.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an kama daliban ne da misalin karfe 2 na dare inda jami’an su ka runtuma cikin dakunan kwanan daliban, Legit ta tattaro.

Kara karanta wannan

Kano: Hukumar Hisbah ta cafke ’yan daudu guda 8 su na tikar rawa da badala a wurin biki

EFCC ta kama dalibai 70 a wani samame a Jami'ar OAU
Jami’an EFCC sun yi ram da wasu dalibai 70 a OAU. Hoto: Ibrahim Lawal, EFCC Nigeria.
Asali: Facebook

Mene dalilin EFCC na kama daliban?

Sai dai har zuwa lokacin tattara wannan rahoro ba mu samu dalilin wannan kame ba da aka yi a Jami’ar da ke Ile-Ife a jihar Osun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban daliban Jami’ar, Abass Ojo ya bayyana cewa an kama daiban guda 72 a dakunansu kuma an tafi da wayoyinsu da motoci.

Wani tsohon shugaban daliban mai suna Joy Abiola ya bayyana wa manema labarai cewa dalibai sun daku sosai kafin kama su, Linda Ikeji ta tattaro.

Mene dalibai ke cewa kan kamen EFCC?

Ya ce:

“Jami’an EFCC sun iso nan da misalin karfe 1:40 zuwa 4:00 wanda iya dalibai ne a wurin, ta yaya za ka kama dalibi don ya mallaki wayar iPhone da mota da kwamfuta?”

Wani dalibi har ila yau, mai suna Ewate ya ce an kwashi mata dalibai yayin kamen, hatta sabbin dalibai da su ka je gaishe da manyansu an kama su, hakan bai dace ba.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi ajalin babban mai sarautar gargajiya, sun sace matarsa, dansa da wasu mutum 8

A cikin wani faifan bidiyo, an gano yadda ake dura daliban a cikin wata motar bas kirar ‘Hummer’ inda ake dukansu su shiga cikin motar.

Mai magana ya yawun hukumar EFCC, a yankin Ibadan, Olumide Egbodofo ya ce za su yi cikakken bayani daga baya.

Shugaban EFCC ya kawo sabuwar doka

A wani labarin, Hukumar EFCC ta kawo sabuwar doka wacce za ta tilasta dukkan ma'aikatan bayyana kadarorinsu.

Shugaban hukumar, Ola Olukayode shi ya bayyana haka inda ya ce shi ma ya bayyana kadarorinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.