Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 1 da Sace Wasu Mutum 25 a Wani Sabon Hari a Kaduna

Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 1 da Sace Wasu Mutum 25 a Wani Sabon Hari a Kaduna

  • Wasu miyagun ƴan bindiga sun kai wani mummunan hari a ƙauyen Ungwan Baka da ke gundumar Agunu a ƙaramar hukumar Kachia ta jihar Kaduna
  • Ƴan bindigan a yayin harin sun halaka mutum ɗaya tare da yin awon gaba da wasu mutum 25 zuwa cikin daji
  • Mazauna ƙauyen sun koka kan yadda miyagun ƴan bindiga suka addabe su da kai hare-hare ba ƙaƙƙautawa

Wakilin Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar fiye da shekara biyar wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi

Jihar Kaduna - Wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun sun kashe wani manomi ɗaya yayin da suka raunata wasu mutum biyu a Ungwan Baka da ke gundumar Agunu a ƙaramar hukumar Kachia ta jihar Kaduna.

Ƴan bindigan waɗanda suka zo da yawansu, sun kai wa mutanen ƙauyen hari ne da sanyin safiyar Talata, 31 ga watan Oktoba, yayin da suka yi awon gaba da aƙalla mutum 25, cewar rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun halaka jami'an yan sanda 3 a wani sabon hari a Zamfara

Yan bindiga sun sace mutum 25 a Kaduna
Yan bindiga sun sace mutum 25 a wani sabon hari a Kaduna Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Yadda ƴan bindigan suka kawo harin

Jaridar Vanguard ta ce wani mutum da ya tsira da ransa, wanda ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"An yi garkuwa da mutum 25 a Unguwan Baka da ke gundumar Agunu a safiyar ranar Talata. Mutane biyu sun jikkata sannan mutum ɗaya ya mutu."
"Mun garzaya da wadanda suka samu raunuka zuwa asibiti, muna musu fatan samun sauƙi, wadanda aka yi garkuwa da su, muna addu'ar Allah ya dawo da su lafiya. Don Allah a samu cikin addu'a. Wannan shi ne hari na uku a kan ƙauyenmu.”

Menene martanin ƴan sanda kan harin?

Sai dai babu wani martani a hukumance daga gwamnatin jihar ko kuma ƴan sanda, domin jami'in hulɗa da jama'a na rundunar jihar, ASP Mansir Hassan bai ɗauki kiran da aka yi masa a waya ba.

Kara karanta wannan

Mayakan Boko Haram sun salwantar da rayukan mutum 16 a wani sabon hari a jihar Yobe

Haka kuma bai dawo da amsa kan saƙon da aka tura masa ta layin wayarsa.

Yan Bindiga Sun Halaka Yan Sanda

A wani labarin kuma, wasu miyagun ƴan bindiga sun kai farmaki kan shingen binciken ababen hawa na jami'an ƴan sanda a jihar Zamfara.

Ƴan bindigan a harin da suka kai kan hanyar titin Funtua zuwa Gusau sun salwantar da rayukan jami'an ƴan sanda uku.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng