Yan Sanda Sun Cafke Yarinya Mai Shekaru 14 Kan Zargin Yi Wa Lakcara Yankan Rago a Jihar Arewa

Yan Sanda Sun Cafke Yarinya Mai Shekaru 14 Kan Zargin Yi Wa Lakcara Yankan Rago a Jihar Arewa

  • 'Yan sanda sun yi nasarar cafke yarinya mai shekaru 14 kan zargin kisan lakcara a jihar Neja
  • Wacce ake zargin mai suna Joy Afekafe ta taba zama 'yar aiki a gidan marigayar na makwanni
  • Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, DSP Wasiu Abiodun shi ya bayyana haka a yau Talata 31 ga watan Oktoba

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Neja - Rundunar 'yan sanda a jihar Neja ta cafke wata yarinya kan zargin hallaka lacrara a jihar.

Yarinyar mai shekaru 14 ana zarginta da yi wa lakcaran da ke koyarwa a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Minna yankan rago, Cewar Tribune.

'Yan sanda sun kama yarinya mai shekaru 14 kan zargin kisan kai
Yan Sanda sun kama yarinya da zargin kisan kai. Hoto: Umar Bago.
Asali: Facebook

Wa ake zargi da hallaka lakcara a Neja?

Kara karanta wannan

Kogi: Jimami yayin da shahararren dan siyasar APC ya riga mu gidan gaskiya awanni kadan kafin zabe

Wacce ake zargin mai suna Joy Afekafe ta taba zama gidan marigayar, Dakta Funmilola Sherifat Adefolalu Dakta a matsayin mai aiki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tsinci gawar Adefolalu a cikin jini a gidanta da ke Gbaiko a bayan garin Minna babban birnin jihar Neja.

Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi 29 ga watan Oktoba yayin mambobin cocinsu su ka kawo mata don duba halin da lakcaran ke ciki.

Wane martani 'yan sanda su ka yi kan lakcarar a Neja?

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, DSP Wasiu Abiodun shi ya bayyana haka a yau Talata 31 ga watan Oktoba a Minna.

Ya ce an kama wacce ake zargin ne a jiya Litinin 30 ga watan Oktoba da misalin karfe 9 na dare a yankin Gbeganu da ke Minna, cewar Leadership.

Ya ce:

Kara karanta wannan

Satar mazakuta: tsagera sun yi wa lakcara dukan kawo wuka a jihar Arewa, 'yan sanda sun fusata

"A ranar Lahadi 29 ga watan Oktoba da misalin karfe 1, wasu abokai da mambobin cocin marigayiyar sun ziyarceta saboda rashin samun wayarta a gidanta da ke Gbaiko a Minna.
"Shigar su ke da wuya su ka samu kakcarar kwance cikin jini da raunuka a tare da ita."

Yayin bincike yarinyar ta tabbatar da cewa ta yi wa lakcarar aiki na makwanni kafin ta kore ta, dalilin haka ya sa ta fadawa 'yan ajinsu abin da ya faru.

Daga bisani 'yan ajin nasu Walex da Smart su ka shirya kisan inda su ka zo har gidan da babur su ka mata duka kuma su ka daba mata wuka har lahira.

An tsinci gawar lakcara cikin jini a jihar Neja

A wani labarin, mutane sun shiga rudani a unguwar Gbaiko da ke Minna a jihar Neja bayan samun gawar wata lakcara.

Marigayiyar mai suna Dakta Funmilola Sherifat lakcara ce a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Minna a jihar Neja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.