Kano: Abba Kabir Ya Ba da Umarnin Tantance Karin Mutane 147 Don Auren Gata, Ya Bayyana Matakin Gaba

Kano: Abba Kabir Ya Ba da Umarnin Tantance Karin Mutane 147 Don Auren Gata, Ya Bayyana Matakin Gaba

  • Gwamnatin jihar Kano na ci gaba da tantancewa tare da duba lafiyar sabbin wadanda za su angwance mutane 147 a jihar
  • Hukumar kare yaduwar cutar kanjamau a jihar, ita ta fara tantancewar don sanin halin lafiyarsu kafin daura mu su aure
  • Idan ba a manta ba, gwamnatin jihar ta dauki nauyin aurarraki 1,800 don rage yawan lalacewar matasa

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano – Gwamnatin jihar Kano ta fara tantance wasu karin mutane 147 da za a daura wa aure a jihar.

Hukumar kare yaduwar cutar sida ita ta fara tantancewar don sanin matakin lafiyarsu kafin daura mu su aure, Legit ta tattaro.

Abba Gida Gida ya umarci tantance karin mutane 1,800 don yi mu su auren gata
An fara tantance mutane 1,800 don yi mu su auren gata a Kano. Hoto: @Imranmuhdz.
Asali: Facebook

Mene dalilin tantancewar a Kano?

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke daliban firamare 2 da cinna wa makarantarsu wuta, an bayyana yadda abin ya faru

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai na hukumar, Usman Datti ya fitar a yau Talata 31 ga watan Oktoba, cewar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Datti ya ce babban daraktan hukumar, Dakta Usman Bashir yayin ran gadi a hukumar ya ce wannan mataki da su ka dauka zai bai wa ma su shirin yin auren damar sanin lafiyarsu da kuma wasu shawarwari.

Daktan ya ce babban makasudin gwaje-gwajen shi ne don ma’auratan su san lafiyarsu saboda kaucewa yaduwar cututtuka bayan anyi aure.

Wane shawara hukumar ta bayar kan tantancewar a Kano?

Ya ce:

“Mu na samun nasarar ce ta hanyar gwaje-gwaje a dakunan mu don dakile wasu matsaloli na lafiya ga ma’auratan.”

Ya ce manyar cututtukan da su ke gwajin a kansu sun hada da cutar kanjamau da ta hanta da sanin kwayar halitta da juna biyu da sauransu.

Kara karanta wannan

Daga Yin Barazanar Tsige Gwamna, Majalisar Dokoki ta Kama da Wuta Cikin Dare a Ribas

Ya kuma bukaci ma su shirin yin auren da su dauki shirin da muhimmanci inda ya ce gwamnatin jihar ta samamr da duk wasu kayan aiki da kwararru don gudanar da shirin a cikin sauki.

Idan ba ku manta ba, gwamnatin jihar ta dauki nauyin aurarraki 1,800 don rage yawan lalacewar matasa da kuma gwauraye, cewar Vanguard.

Abba Gida Gida ya dauki nauyin aurarraki 1,800 a Kano

A wani labarin, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jagoranci daura auren ma’aurata 1,800 da gwamnatin jihar ta dauki nauyi.

Jagorar siyasar jihar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso shi ma ya samu halartar auren tare da sanya albarka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.