Gwamna Dauda Ya Cigaba da Tona Yadda Gwamnatin Matawalle ta Wawuri Dukiyar Zamfara
- Gwamnatin Zamfara ta bankado yadda Bello Matawalle ya amince da kwangilar gina gidan gwamna a kowace karamar hukuma
- Dauda Lawal Dare ya ce gwamnatin da ta shude ta biya kusan duka kudin kwangilar a lokacin da ba a kai ga fara ayyukan ba
- Sabon Gwamnan jihar ya huro wuta cewa dole kamfanonin da aka biya wadannan kudi su dawo da dukiyar al’umma da aka karkatar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Zamfara - Gwamnatin jihar Zamfara ta fito da hujjoji da ke nuna yadda Bello Matawalle ya karkatar da kudi da nufin gina gidajen gwamna.
The Cable ta ce kafin a kammala kwangilar har Bello Matawalle ya amince a biya 100% na na sama da N1bn da aka ware na wannan aikin.
An karkatar da kudin gina katanga da sayen kayan dakin gidajen da gwamna zai rika zama idan ya kai ziyara a duka kananan hukumomi 14.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wani jawabi da Mai magana da yawun gwamna, Sulaiman Bala Idris ya fitar a ranar Lahadi, ya dage da tona asirin gwamnatin da ta wuce.
A madadin Mai girma Dauda Lawal Dare, Kakakin ya ce ana wayar da kan Zamfarawa kan facaka da aka yi da kudinsu a karyar kwangila.
"Ya sabawa ka’idar aikin gwamnati a biya duka kudin aikin kwangilar da ba a fara ba; akwai ka’idojin da aka yi watsi da su da gan-gan.
Dole mu hukunta wadanda su ka bada kwangilolin bogi su ka biya kudi, kuma mu karbo abin da yake hakkin mutanen jihar Zamfara ne."
- Sulaiman Bala Idris
Yadda aka fitar da kudin kwangiloli a Zamfara
Sulaiman Bala Idris ya ce kudin kwangilar gidajen sun bambanta a kowace karamar hukuma, amma galibi an fitar da 90% na kudin aikin.
Jaridar Pulse ta ce takardun sun nuna an biya ₦1,966,035,160.00 ga kamfanin BES BELMON Nigeria Limited a ranar 27 ga Disamban 2021.
‘Yan kwangila da ke aiki a K/Namoda, Zurmi, Bakura, Maradun, Bukkuyum, Bungudu da Gummi sun samu duka kudin kafin a fara yin komai.
Gwamnatin Zamfara ta bukaci kamfanin BES BELMON Nig. ya dawo da kudin da ya karba.
Matawalle ya saci dukiyar gwamnati?
Kwanaki Dauda Lawal ya fito da bayanai da za su gaskata zargin da yake yi wa Bello Matawalle, har yanzu Ministan bai fito ya wanke kan shi ba.
Dauda ya nuna hujjoji da za su nuna Matawalle ya biya N3,465,569,736.90 da N2,310,379,824.60 a kan aikin filin jirgin sama da bai yi nisa ba.
Asali: Legit.ng