Gwamnatin Dauda Ta Fallasa ‘Facakar’ da Ministan Tinubu Ya Yi a Lokacin Ya na Gwamna

Gwamnatin Dauda Ta Fallasa ‘Facakar’ da Ministan Tinubu Ya Yi a Lokacin Ya na Gwamna

  • Gwamnatin jihar Zamfara ta maidawa Muhammad Bello Matawalle martani a game da zargin yin sama da fadi da dukiyar al’umma
  • Mai magana da yawun Gwamna mai-ci, Sulaiman Bala Idris ya fitar da jawabi dauke da yadda aka rika facaka da baitul-malin Zamfara
  • An fitar da makudan biliyoyi da nufin yin filin jirgin sama, duk da kudin da aka kashe a kwangilar, ana zargin wannan aiki bai je ko ina ba

Zamfara - Gwamnatin jihar Zamfara ta fitar da hujjoji da ta ke ganin za su tabbatar da zargin da ta ke yi wa gwamnatin Bello Matawalle.

The Cable ta ce bayanan da aka fitar sun nuna yadda tsohuwar gwamnatin APC ta yi bindiga da makudan kudi a kwangilar filin jirgin sama.

Bello Matawalle wanda shi ne karamin Ministan tsaro a Najeriya ya yi kokarin musanya zargin a lokacin da aka fara jifansa da laifin.

Kara karanta wannan

Mun Toshe Hanyar Sata, Mai Niyyar Cin Kudi Ya Bar Gwamnatinmu - Abba Gida Gida

Gwamnatin Dauda
Gwamnan Zamfara Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

Gwamna Dauda ya taso Matawalle a gaba

Amma a wani jawabi da mai magana da yawun gwamna Dauda Lawal Dare ya fitar a yammacin ranar Lahadi, ya yi karin bayani a kan zargin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da yake magana a garin Gusau, Malam Sulaiman Bala Idris ya ce Matawalle ya jawo za a bankado danyen aika-aikar da ya tafka a ofis.

Sulaiman Bala Idris yake cewa halin da jihar Zamfara ta samu kan ta a yau, a sakamakon abubuwan da gwamnatin Matawalle ta yi ne.

Badakalar N1bn da tashar jirgi a Zamfara

Rahoton ya ce Dauda Lawal Dare ya zargi magabacinsa da umartar ma’aikatar kananan hukumomi ta cire N1bn daga asusun hadaka.

Mai girma Gwamnan ya ce daga cikin kudin, an biya N825m ga ‘yan kwangila ba tare da bin ka’ida ko bayanin abin da aka yi da dukiyar ba.

Kara karanta wannan

Hakikanin Abin da Ya Faru – Gwamna Ya Yi Bidiyon Karyata 'Harin' da Aka Kai Masa

Gwamnatin Dauda ta ce badakalar N11bn da aka tafka wajen gina filin jirgi kadan ne a kan sauran barnar da aka yi da sunan kwangiloli.

Zargin da ake yi wa Matawalle

Tun farko an zaftare kudin kwangilar daga N28bn zuwa N11bn, Sun ta rahoto gwamnatin Zamfara ta na cewa da alamar tambaya.

Tashin farko aka biya ‘yan kwangila 30% (N3,465,569,736.90) ba tare da an amince da aikin ba, daga baya aka kara masu N2,310,379,824.60.

An biya wadannan N2.3bn ne da sunan bashi, gwamnati ta ce ba a bi dokokin da tsari ba.

Nadin sabon shugaban EFCC

Olanipekun Olukoyede ya fara mulki da matsala, ana yi wa kujerarsa barazana a EFCC domin an ji labari an je kotu domin ganin an tsige shi.

Masu shigar da karar sun hada da Bola Tinubu, Godswill Akpabio da Sakataren EFCC a kotu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel