Ana Shigowa Babu Gayyata, Shugaban Kasa Ya Takaita Taron FEC ga Jami’an Gwamnati 4

Ana Shigowa Babu Gayyata, Shugaban Kasa Ya Takaita Taron FEC ga Jami’an Gwamnati 4

  • Bola Ahmed Tinubu ya gargadi jami’an gwamnatin tarayya su daina zuwa wajen zaman FEC idan dai ba a gayyace su ba
  • Bayan shugaban kasa da mataimakinsa, wadanda doka ta ba hurumin halartar taron su ne Ministoci da sakataren gwamnati
  • Tinubu ya yi wa wasu daga cikin Sakatarori da Hadimansa izinin shigowa FEC, bayan su babu wanda za a budewa kofa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya ja-kunnen mutane game da halartar taron FEC a fadar Aso Rock ba tare da an gayyace su ba.

Shugaban Najeriyan ya ce akwai wadanda ba su da hurumi da ke shigowa fadar shugaban kasa idan ana zaman majalisar zartarwa (FEC).

Kara karanta wannan

Hukuncin kotun koli: A karshe Tinubu ya maida martani ga kalaman Atiku Abubakar

The Cable ta ce shugaba Bola Tinubu ya yi wannan magana kafin a fara taron FEC a jiya bayan an canza ranar zaman daga duk Laraba.

Shugaban kasa
Shugaban kasa, Bola Tinubu a taron FEC Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bola Tinubu ya yi wannan gargadi ne bayan ganin hoton yaronsa a cikin taron.

A kowace Litinin, Ministocin tarayya da sauran manyan mukarraban gwamnati su na zama domin a tattauna a babbar majalisar tarayyar.

Umarnin da Bola Tinubu ya bada

"A wancan makon, na lura mutane su na shigowa su na fita daga majalisar nan (FEC).
Mutane su na shigowa nan yayin da bai dace su shigo ba. Ba za a amince da wannan ba.
A nan zan sanar da ku mutanen da ya kamata su kasance a nan.

Su wanene za a bari su shigo FEC?

Mai bada shawara kan gudanar da tsare-tsare, Hadiza Bala Usman, Mai bada shawara wajen yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, Babban Sakatare, Hakeem Muri-Okunola da Sakatare, Damilotun Aderemi.

Kara karanta wannan

Tinubu zai canja shugaban ma'aikatan fadarsa, Gbajabiamila? Shugaban Kasa ya magantu

Wadannan su ne mutanen da aka ba izini su shigo nan idan mu na tattauna a kana bin da ya shafi kasa.

Idan har ban gayyace ka ba, ka da ka zo."

- Bola Tinubu

Tinubu ya kare Femi Gbajabiamila

21st Century Chronicle ta ce shugaban kasa ya umarci Sakataren gwamnati da shugaban ma’aikatan gwamnati su tabbata an bi umarnin.

Bola Tinubu ya kuma bukaci a rika yin taron cikin tsari, ya kuma tabbatarwa kowa cewa ya na tare da hadiminsa, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila.

FEC ta zauna sau 4 bayan nada Ministoci

A makonnin baya aka ji labari an rantsar da Dr. Jamila Bio, Ayodele Olawande da Balarabe Abbas Lawal, sun shiga ofis a matsayin ministoci.

Majalisar FEC mai alhakin zartarwa za tayi zama hudu a karkashin jagorancin Bola Tinubu, a nan ake amincewa da dokoki da tsare-tsaren kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng