Abun Farin Ciki Yayin da Tagwayen Kano Da Ke Hade Suka Tafi Saudiyya Don Ayi Masu Aiki

Abun Farin Ciki Yayin da Tagwayen Kano Da Ke Hade Suka Tafi Saudiyya Don Ayi Masu Aiki

  • Tagwayen da aka haifa a hade a jihar Kano sun bar Najeriya domin yi masu tiyasa a kasar Saudiyya
  • Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya sallame su tare da da yi masu fatan nasara a aikin da za a yi masu
  • Abba gida gida ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa daukar nauyin aikin ya nuna alaka mai karfi da ke tsakanin jihar Kano da kasar Saudiyya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullun

Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya sallami tagwayen da aka haifa a hade yayin da suka lula kasar Saudiyya domin ayi masu aiki.

Abba gida gida ya bayyana cewa gwamnatin kasar Saudiyya ce ta dauki nauyin aikin nasu.

Kara karanta wannan

Jerin sunayen gwamnoni da suka yi wa iyayen gidansu a siyasa karan-tsaye

Za a yi wa tagwayen Kano tiyasa a Saudiyya
Abun Farin Ciki Yayin da Tagwayen Kano Da Ke Hade Suka Tafi Saudiya Don Ayi Masu Aiki Hoto: @Kyusufabba
Asali: Twitter

Ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X (wacce aka fi sani da Twitter a baya) @Kyusufabba, a ranar Litinin, 30 ga watan Oktoba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya ce wannan karamcin ya nuna alakar da ke tsakanin jihar Kano da kasar Saudiyya.

Ya rubuta:

"A yau, mun yi bankwana da tagwayen da ke hade wadanda suka lula zuwa kasar Saudiyya don ayi masu tiyata.
“Gwamnatin Saudiyya a karkashin jagorancin Sarki Salman Bin Abdulaziz ce ta dauki nauyin tiyatar, kuma wata kwakkwarar bayani ne kan alakar da ke tsakanin jihar Kano da masarautar Saudiyya.
"Ina yi masu fatan nasara a tiyatar."

Abba ya biya kudin asibitin Asmau Sani

A wani labarin, Legit Hausa ta rahoto a baya cewa gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya dauki nauyin jinyar wata yarinya da ke fama da ciwon daji.

Kara karanta wannan

Atiku: Kotun koli ta halasta haram da kirkirar takardar bogi

Yarinyar mai suna Asmau Sani na fama da ciwon daji wacce ta ke kwance a asibitin Dala da ke jihar Kano.

Gwamna Abba ya biya kimanin naira miliyan 1.5 don yi wa wannan yarinyar aiki da kuma karin naira dubu 200 don siya mata abinci.

Ma'aikata sun garkame majalisar Kano

A wani labari na daban, mambobin ƙungiyar ma'aikatan majalisar dokoki ta Najeriya (PASAN) reshen jihar Kano, sun garƙame zauren majalisar dokokin jihar Kano ranar Litinin.

Ma'aikatan sun ɗauki wannan mataki ne yayin da suka bi sahu, suka tunduma yajin aikin sai baba ta gani, wanda ƙungiyarsu ta ƙasa ta ayyana shiga a faɗin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng