Tashin Hankali Yayin da Jami'an Tsaro Suka Yi Harbi Kan Gwamna Fubara Na Rivers

Tashin Hankali Yayin da Jami'an Tsaro Suka Yi Harbi Kan Gwamna Fubara Na Rivers

  • Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara, yayi jawabi ga magoya bayansa dangane da shirin tsige shi da ake yi
  • A ranar Litinin ne Fubara ya yi Allah-wadai da cewa bai yi wani laifi ba wanda zai sanya majalisar dokokin jihar ta tsige shi
  • Sai dai, ya yi zargin cewa an haɗa baki da jami'an tsaron jihar domin sai da suka harbe shi kai tsaye

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wakilin Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar fiye da shekara biyar wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi

Portharcourt, jihar Rivers - Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers, ya yi magana dangane da dambarwar siyasar da ta dabaibaye jihar.

Hakan na zuwa ne bayan da ƴan majalisar dokokin jihar suka fara yunƙurin tsige shi daga muƙaminsa.

Gwamna Fubara ya zargi jami'an tsaro
Gwamna Fubara ya zargi jami'an tsaro da harbinsa kai tsaye Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Fubara ya ce jami'an tsaro sun harbe shi kai tsaye

Kara karanta wannan

Majalisar dokokin jihar Rivers ta mika wa gwamna Fubara takardar shirin tsige shi

Da yake jawabi ga wasu magoya bayansa a harabar majalisar a safiyar ranar Litinin, 30 ga watan Oktoba, gwamnan ya yi zargin cewa an haɗa baki da hukumomin tsaro, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya yi magana ne bayan da aka tsige Edie Edison, babban na hannun damansa, a matsayin shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar Rivers.

Gwamnan, wanda ya ce bai aikata wani laifin da zai sa a tsige shi ba, ya nemi waɗanda ke ƙoƙarin ganin bayansa da su fito fili, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

A kalamansa:

"Daga abin da na gani hukumomin tsaro ma an haɗa baki da su. Suna ta harbi na kai tsaye amma ba komai, wata rana wani zai mutu."
"Lokacin da mutane a nan suke tambayar wanene wannan Fubara? Shi ne mutumin da aka kashe saboda gwagwarmayarsa. Ba na gaba da kowa. Ba na shirya wani abu a kan kowa, sannan ban san daga ina waɗannan abubuwan suke fitowa ba."

Kara karanta wannan

Maganar tsige Gwamnan Ribas ta yi nisa, an sauke masoyinsa daga kujerar Majalisa

Gwamna Fubara na takun saƙa da Wike

Rahotanni sun bayyana cewa Fubara yana takun saƙa ne da magabacinsa kuma ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike.

Sai dai, Abdul Rasheeth, mai taimakawa tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar kan harkokin yada labarai, ya bayyana cewa Gwamna Fubara da magabacinsa, Wike, sun yi ta kai ruwa rana a makon da ya gabata.

Shirin Tsige Gwamna Fubara Ya Yi Nisa

A wani labarin kuma, majalisar dokokin jihar Rivers, ta miƙa wa gwamna Siminalayi Fubara, takardar fara shirin tsige shi.

Majalisar ta miƙa wa gwamnan takardar shirin tsige shi daga muƙaminsa, a safiyar ranar Litinin, 30 ga watan Oktoban 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng