Abba Gida Gida Ya Kai Ziyara Asibiti, Ya Ba da Miliyan 1.5 Na Jinya Ga Yarinya, Asmau Sani
- Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya kai ziyarar bazata asibitin Dala don ganin halin da yarinya Asmau Sani ke ciki
- Asmau Sani wata na fama da ciwon daji wanda aka yi ta yada rashin lafiyar tata a kafafen sadarwa
- Abba Kabir yayin kai ziyarar ya ba da gudunmawar naira miliyan 1.5 inda ya ce zai ci gaba da kulawa da kuma bibiyar rashin lafiyar
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano – Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba KLabir Yusuf ya dauki nauyin jinyar wata yarinya da ke fama da ciwon daji.
Yarinyar mai suna Asmau Sani na fama da ciwon daji wacce ta ke kwance a asibitin Dala da ke jihar Kano.
Wane gudunmawa Abba Kabir ya bayar a asibitin Kano?
Gwamna Abba ya biya kimanin naira miliyan 1.5 don yi wa wannan yarinyar aiki da kuma karin naira dubu 200 don siya mata abinci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Idan ba a mantaba, an yi ta yada rashin lafiyar Asmau Sani a kafafen sada zumunta inda wani bawan Allah ya biya mata kudin aiki naira 408 tare da yin alkawarin wasu karin kudade.
Abba Kabir ya yi wannan taimako ne bayan kai ziyara asibitin da yarinyar ke kwance inda ya nuna damuwarshi ganin irin halin da ta ke ciki.
Wane martani Abba Kabir ya yi a asibitin Kano?
Ya ce wannan rashin lafiyan Asmau ya dauki hankalinsa ne a kafar sadarwa inda ya yi amfani da wannan damar don kai mata ziyara da kuma ba da taimako.
Gwamnan ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter a jiya Lahadi 29 ga watan Oktoba.
Ya kara da cewa za su ci gaba da bibiyar yarinyar don sanin halin da take ciki da sauran marasa lafiya a jihar wanda shi ne su ka fi bai wa kulawa.
Abba Kabir ya dauki nayin karatun dalibai 1001
A wani labarin, Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya dauki nauyin dalibai 1001 zuwa kasashen Indiya da Uganda don karo karatu.
Gwamna ya dauki wannan matakin ne don bin sawun tsohon gwamna kuma uban gidansa, Rabiu Musa Kwankwaso.
Kason farko na daliban 550 sun tashi zuwa kasar Indiya a ranar Juma’a 20 ga watan Oktoba.
Asali: Legit.ng