Yajin Aiki: Kungiyar Kwadago Ta Ba Gwamnatin Tarayya Sabon Sharadi Domin Halartar Zaman da Za Su Yi

Yajin Aiki: Kungiyar Kwadago Ta Ba Gwamnatin Tarayya Sabon Sharadi Domin Halartar Zaman da Za Su Yi

  • Ƙungiyar kwadago ta ƙasa (NLC) ta ba gwamnatin tarayya sharaɗi na halartar taron tattaunawar da za su yi
  • Shugaban NLC, Joe Ajaero ya ce ƙungiyar za ta ƙi halartar ganawar da za su yi da gwamnatin tarayya a ranar Litinin idan Simon Lalong zai kasance a wajen taron
  • Ajaero ya zargi ministan ƙwadago da samar da ayyukan yi da saba yarjejeniyar da aka ƙulla tsakanin ɓangarorin biyu

FCT, Abuja - Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) ta yi barazanar ƙin halartar ganawar da za ta yi da gwamnatin tarayya idan ministan ƙwadago da samar da ayyukan yi, Simon Lalong zai halarci taron a ranar Litinin, 30 ga watan Oktoba.

Shugaban ƙungiyar ta NLC, Joe Ajaero ne ya bayyana haka yayin da yake jawabi ga manema labarai a Abuja, kan halin da ma'aikatan jihar Imo ke ciki a ranar Lahadi, 29 ga watan Oktoba, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kotun Koli: Babban Malamin Addini Ya Yi Hasashen Abin da Zai Faru Bayan Yanke Hukunci

NLC ta yi barazanar kin halartar taro da FG
Joe Ajaero ya ce ba za su halarci zama da FG ba idan Lalon zai halarci zaman Hoto: @NLCHeadquarters
Asali: Twitter

Ajaero ya ce NLC ta ɗauki wannan matakin ne saboda saɓa yarjejeniyar da ministan ya yi kan rigimar da ke tsakanin mambobin ƙungiyar ma'aikatan sufuri ta ƙasa (NURTW).

Meyasa NLC ba za ta halarci zama da FG ba?

Kamar yadda Daily Trust ta rahoto, ya zargi Lalong da goyon bayan wani ɓangare cikin rigimar saɓanin yarjejeniyar da suka cimma kan lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

"Da fatan za mu iya ganawa a ranar Litinin da gwamnatin tarayya domin ganin ko an cimma yarjejeniya da kungiyoyin ƙwadago kan kayan tallafin cire man fetur ko ba haka ba."
"Idan har za a yi wannan taron, zai kasance ba tare da ministan ƙwadago da samar da ayyukan yi ba, saboda ba za mu halarci duk wani taro da gwamnatin tarayya da ministan ƙwadago zai halarta ba."
"Za ku iya tunawa cewa matsayar da muka cimma kan ƙungiyar ma'aikatan sufuri ta kasa (NURTW) ita ce duk ɓangarorin, waɗanda suka haɗa har da ƴan sanda su dakata har sai an warware rikicin amma hakan bai faru ba."

Kara karanta wannan

Atiku Ya Halarci Taro Na Musamman Bayan Hukuncin Kotun Koli, Ya Sanya Hotuna

"Domin haka duk wani taro da za mu yi da gwamnatin tarayya, ba za a yi shi tare da ministan ƙwadago da samar da ayyukan yi ba."

Kungiyoyin Kwadago Sun Ba Gwamnoni Sabon Wa'adi

A wani labarin kuma, ƙungiyoyin ƙwadago sun ba gwamnonin jihohi 36 sabon wa'adi kan ƙarin albashin N35,000 ga ma'aikata.

Ƙungiyoyin sun ba gwamnonin wa'adin mako biyu domin fara tattaunawa kan yadda za su fara biyan ma'aikatansu ƙarin albashin bayan yarjejeniyar da aka cimma da gwamnatin tarayya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng