An Yi Ruwan Daloli, Bidiyo Ya Nuna Yadda Attajiri Ya Hau Jirgi Ya Sako Kudi, an Yi Warwaso

An Yi Ruwan Daloli, Bidiyo Ya Nuna Yadda Attajiri Ya Hau Jirgi Ya Sako Kudi, an Yi Warwaso

  • Wani shahararren dan soshiyal midiya ya watsa dala miliyan 1 kuma ya baiwa mutane damar tsintar kudin kamar wake a gona
  • Mutumin mai suna Kazma Kamitch, ya saki kudin ne daga wani jirgin sama mai saukar ungulu da ke shawagi a saman garin Lysa Nad Lahem na Jamhuriyar Czech
  • A cikin wani faifan bidiyo da ya yadu, Kazma ya ce abin da ya yi shi ne ruwan samamn kudi na gaske na farko a duk duniya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

Czech - Wani mutum ya shiga kanun labarai bayan da ya hau saman jirgi da kudade tare da sako su kamar ruwan sama don mutane su dauka.

A cikin wani faifan bidiyon da aka yada a kafar sada zumunta, mutumin mai suna Kazma Kazmitch, ya ce abin da ya yi na nufin ruwan saman kudi na gaske da aka fara yi na farko a duniya kenan.

Kara karanta wannan

Ya kamata CBN ta sa a daina amfani sabbin takardun Naira da Buhari ya kawo, malami ya fadi dalilai

A bidiyon, Kazam ya saki dala miliyan 1 daga cikin jirgin sama mai saukar ungule a garin Lysa Nad Lahem na Jamhuriyar Czech.

Yadda wani matashi ya yi ruwan kudi
Ruwan kudi ya jawo cece-kuce | Hoto: @kazma_kazmitch
Asali: TikTok

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai kawai gani aka yi kudaden sun watse a sama suka nufi kasa, inda jama'a suka taru a can suna jiran sauka su kwashi banza.

Mutane sun taru don cin banza

Jiragen sama masu saukar ungulu uku ne suka yi shawagi a sama, amma daya ne kadai ya sako kudaden daga cikin wani kwando da ke makale a jikin igiya.

Da aka bude kwandon, sai kawai suka watse kamar ganye. Da yawa daga cikin magoya bayansa sun zo wurin da jakunkuna, kuma sun taimaki kansu ta hanyar tsintar rabonsu.

Sai dai, ba kowa ne ya samu damar samun halartar wannan garabasa ba, domin kuwa zaba aka yi ta sakon email da ya turawa mabiyansa.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka tsohon shugaban karamar hukuma a Benue bayan sace shi na kwanaki

Kalli bidiyon:

Ga dai martanin jama’a a kafar sada zumunta

@kayagtyvlt1 ya tambaya:

"Yaushe zaku zo Uganda?"

@Roaming Julius ya ce:

"A Uganda, ba za ku tsinci komai ba. Museveni zai yanke dukkan yankin."

@Savilito ya ce:

"A Najeriya, kafin ma kudin su sauko kasa tuni sun kare a iska.”

An yi irin wannan a Amurka

A wani labarin, wata motar kudi a Amurka ta haifar da wani babban al'amari yayin da daya daga cikin kofofinta ta bude kuma kudade daloli masu yawa suka watse a kasa.

Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, 19 ga watan Nuwamba, inda ya kawo tsaiko ga cunkoson jama’a a California, yayin da jama’a ke tururuwa domin kwasar rabonsu.

Da take nadar bidiyon lamarin, wata budurwa mai suna Demi Baby a shafin Instagram ta ce wannan shi ne mafi girman abin mamaki da ta taba gani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.