Ruwan kudi a shagalin bikin Hanan Buhari ya janyo cece-kuce (Bidiyo)
Bidiyon yadda ake ruwan kudi a bikin diyar shugaban kasar Najeriya, Hanan Buhari da Turad Sha'aban, ya janyo cece-kuce a kafafen sada zumuntar zamani.
Wannan bidiyon ya bayyana ne bayan a kalla watanni biyu da bidiyon dan antoni janar kuma ministan shari'a, Abdulazeez Malami, ya bayyana inda ya yi aure kuma aka dinga watsi da Naira a jihar Kebbi.
A bidiyon, an ga angon da amarya tare da jama'a da yawa sun watsa musu kudi. Duk da ba sabon abu bane mannawa mutum kudi a biki, babban bankin Najeriya ya hana wannan lamari a sashi na 21 na dokokinsa na 2007. Hakan zai iya sa a ci tarar mutum N50,000 ko daurin watanni shida a gidan maza
A saboda wannan dokar ta babban bankin Najeriya, 'yan sanda sun saba kama jama'a da ke siyar da sabbin kudade a wuraren bukukuwa.
Amma kuma wasu 'yan Najeriya sun ce abun takaici ne da kunya ta yadda ake watsi da kudi a wurin bikin da aka yi a fadar shugaban kasar.
A tsokacin da wani ya yi mai suna Sylvester Grassland a Facebook, ya ce, "A lokacin da suke manna kudi, a tsare suke. Amma a lokacin da wani na daban ne yayi, ba ya mutunta naira."
KU KARANTA: Hotuna da bidiyon ranar daurin auren Hanan Buhari da Turad Sha'aban
Benjamin Ebeshi duk a Facebook kuwa cewa yayi, "Lika naira a fadar shugaban kasa? Me ya faru da dokokin babban bankin Najeriya da ya haramta hakan? Jama'a marasa bin doka."
Dare Olowookore ya ce, "watsa kudi babban laifi ne. CBN tana kashe miliyoyin naira a kowacce shekara wurin wayar da kan jama'a. Amma kuma ga iyalan farko na Najeriya suna yi.
"Ta yuwu gwamnan babban bankin Najeriyan bai samu damar halarta ba. A gaskiya wannan shine ake kira take dokar kasa kai tsaye."
Babatunde Alexander Michael ya wallafa cewa, "darasin koyo a nan: Kada ka kafa doka idan ba za ka iya bin ta ba. A watan Oktoban 2018 babban bankin ya sanar da cewa duk wanda ya lika naira a biki za a dauresa ko a ci shi tara."
Amma kuma wasu 'yan Najeriya sun karesu, inda suka ce wannan dama can ana saba yi a bukukuwa.
Sun ce duk da hakan karantsaye ne ga dokar babban bankin Najeriya, ba wani babban laifi bane don haka a barsu su wataya.
Baffa Garba ya rubuta, "Ban ga wani abun laifi a nan ba. Naira ce kawai kuma 'yan dari bibbiyu ne nake gani. Ko a bikin talaka ana manna su. Dukkansu 'yan dangi ne kuma 'yan uwa da abokan arziki za su iya mannawa."
Wani mai tsokacin Njinma Sharon cewa yayi, "Ko a bikin talakawa ana manna kudi, toh ka duba wannan gidan manyan. Bani da matsala idan sun watsa kudi, amma kada ya zama handamosu aka yi."
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng