An Shiga Rudani Yayin da Aka Tsince Gawar Lakcara a Jami’ar Neja, an Mata Yankan Rago
- An bayyana yadda wata mata malamar jami'a ta rasa ranta a cikin gidanta da ke birnin Minna a jihar Neja
- An tsinci gawar matar bayan da aka yi mata yankan rago a cikin gidanta, lamarin da ya dauki hankali sosai
- Ba wannan ne karon farko da ake hallaka mata a cikin gidajensu ba a Najeriya, hakan ya sha faruwa a baya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.
Minna, Neja - An tsince gawar wata lakcara a Jami'ar Fasaha ta Tarayya da ke Minna a jihar Legas, Dr. Adefolalu Funmilola Sherifat bayan an yi mata yankan rago a gidanta da ke Gbaiko a birnin.
Shugaban kungiyar malaman jami'a ta ASUU a jami'ar, Farfesa Gbolahan Bolarin ya tabbatar da aukuwar wannan lamari ga kafar yada labarai ta Channels Tv.

Source: UGC
A cewar Farfesa, an gano gawar tata ne a ranar Lahadi da safe a lokacin da mambobin cocinsu suka biyo gidanta bayan gane bata zo coci ba a makon nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka gano mutuwarta
A cewar wasu mazauna yankin, bayan bude kofar gidan da karfi, an ganta kwance cikin jini tare da wuyanta a yanke ga kuma wuka a gefenta.
A halin da ake ciki, 'yan kira 'yan sandan yankin don daukar gawarta zuwa dakin ajiye gawarwaki a asibiti mafi kusa a yankin.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Wasiu Abiodun ya shaidawa Channels Tv cewa, za a sanar da 'yan jarida duk wani sakamako na bincike game da mummunan lamarin.
Waye mijin mamaciyar?
Wasu mazauna yankin sun bayyana cewa, mijin malamar mai koyarwa a jami'a, wanda shi ma a lakcara kafin mutuwarsa ya riga ta rasu tun can baya.

Kara karanta wannan
Uba Ya Shiryawa Diyarsa Kasaitaccen Biki Na Dawowarta Gida Bayan Mutuwar Aurenta, Bidiyon Ya Yadu
Ya zuwa rasuwarta, an ce tana rayuwa ne da 'yar aiki, amma ta sallame ta a ranar Juma'ar da ta gabata kafin rasurwata, inji 'yan unguwar.
An kama wanda ya kashe mata a gidanta
A wani labarin mai kama da wannan, tuni 'yan sanda suka kama wani matashin da ake zargin ya yiwa dattijuwa kisan gilla a wani yankin jihar Gombe.
A rahoton da muka kawo maku a baya, an bayyana yadda aka tsinci gawar wata mata kwance cikin jini a dakinta bayan yi mata kisan gilla.
Hankali ya tashi, 'yan sanda sun yi binciken da ya kai ga gano wanda ya aikata mummunan aikin cikin mako guda.
Asali: Legit.ng
