Ba Ni Na Yi Nasara Ba, Dimokradiyya Ta Yi Nasara, Cewar Fintiri Bayan Lallasa Binani a Kotu
- Bayan nasara a kotu, gwamna Fintiri ta fito ya yi magana mai daukar hankali game da zaman da aka yi a kotu
- Ya ce wannan nasara ce ga dimokradiyya ba kawai shi kadai ba, duba da yadda aka bi dokar kasa
- Tun bayan kammala zaben gwamna aka shiga kai ruwa rana tsakanin 'yan takara a kotunan zabe
Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.
Yola, Adamawa - Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa ya bayyana nasarar da ya samu a kotun sauraron kararrakin zaben gwamna a matsayin "nasara ga dimokradiyya da bin doka da oda".
Fintiri ya bayyana haka ne jim kadan bayan da kotun ta yi watsi da karar Aishatu Binani ta APC tare da alanta shi a matsayin wanda ya lashe zaben bana a ranar Asabar, Daily Nigerian ta ruwaito.
A baya, rahotanni sun bayyana yadda Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta bayyana Fintiri a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna bayan kammala kada kuri'u da aka yi a ranar 18 ga Afrilu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda batun ya faro tun farko
‘Yar takarar gwamna a jam’iyyar APC, Aishatu Binani, ta shigar da kara tana kalubalantar zaben, inda ta ce ba a gudanar da zaben bisa ka’ida da dokar zabe ba.
Da yake mayar da martani, Fintiri ya bada tabbacin gudanar da kyakkyawan shugabanci ga al’ummar jiharsa, Ripples Nigeria ta ruwaito.
A cewarsa, wannan nasara ba komai bace face kara tabbatar da bin tafarkin dimokradiyya da kuma doka da oda a kasar nan.
Ku ba mu wuri mu yi aiki - Fintiri
Fintiri ya yi kira ga wadanda suka maka shi a kotu kan su koma gefe domin ci gaban jihar da kuma kasa baki daya.
Ya kuma yabawa alkalan kotun bisa rawar da suka taka wajen tabbatar da gaskiya da adalci a aikinsu na hukunci.
Daga karshe, ya yabawa tawagar lauyoyi da ‘yan jarida da kuma kungiyoyin fararen hula bisa rawar da suka taka tun daga lokacin zabe har zuwa lokacin da kotun ta yanke hukunci.
Yadda aka kori karar Binani
A wani labarin, kotun zaben gwamnan jihar Adamawa a ranar Asabar 28 ga watan Oktoba ta tabbatar da sake zaben Umaru Fintiri a matsayin zababben gwamnan jihar a zaben gwamnan da aka yi a watan Maris din bana, Channels Tv ta ruwaito.
Bayan zaben gwamnan Adamawa da ya janyo cece-kuce, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana Fintiri a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar a karo na biyu.
Asali: Legit.ng