Allah Ya Yi Wa Ohinoyi na Kasar Ebira Ado Ibrahim Rasuwa a Asibitin Abuja

Allah Ya Yi Wa Ohinoyi na Kasar Ebira Ado Ibrahim Rasuwa a Asibitin Abuja

  • Ohinoyi na kasar Ebira, Dr Ado Ibrahim, ya rasu yana da shekaru 94 a wani asibitin Abuja inda yake jinyar rashin lafiya da ta shafi tsufa
  • Dr. Ado Ibrahim, wanda ya kasance shahararren dan kasuwa ya hau kujerar sarauta a 1997 bayan mutuwar Ohinoyi Sanni Omolori na daular Oziada
  • A shekarar 2022 ne gwamnatin jihar Kogi ta tsitsiye marigayi sarkin bisa zargin rashin mutunta tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamna Yahaya Bello

Babban birnin tarayya, Abuja - Allah ya yi wa Ohinoyi na kasar Ebira, Dr Ado Ibrahim, rasuwa yana da shekaru 94 a duniya.

Kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto, babban basaraken na kasar Ebira ya koma ga mahaliccinsa a safiyar ranar Lahadi, 29 ga watan Oktoba.

Basaraken kasar Ebira
Allah Ya Yi Wa Ohinoyi na Kasar Ebira Ado Ibrahim Rasuwa a Asibitin Abuja
Asali: Twitter

An tattaro cewa mataimakin shugaban kungiyar sarakunan gargajiya na jihar Kogi ya rasu a wani asibitin Abuja yayin da yake jinyar rashin lafiya mai alaka da tsufa.

Kara karanta wannan

Majalisar Wakilai Ta Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Gwanjar da Barikokin ’Yan Sanda, Ta Bayyana Kwararan Dalilai

Za a yi jana'izar basaraken mai daraja ta daya a yau Lahadi a garin Okene daidai da koyarwar addinin Musulunci, rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit Hausa ta lura cewa fadar Ohinoyi da gwamnatin jihar Kogi basu riga sun sanar da batun mutuwar basaraken ba a hukumance.

Ohinoyi na kasar Ebira: Wanene Dr Ado Ibrahim?

Dr Ado Ibrahim ya kasance shahararren dan kasuwa wanda ya shafe yawancin rayuwarsa a Lagas kafin ya zama Ohinoyi na kasar Ebira.

Ya hau kujerar sarautar Ohinoyi na kasar Ebira bayan rasuwar Ohinoyi Sanni Omolori na gidan Oziada a 1997.

An haifi marigayi sarkin ne a ranar 7 ga Fabrairu, 1929. Ya yi karatun boko da na addini.

Yadda gwamnatin Kogi ta tsitsiye Ado Ibrahim

A baya Legit Hausa ta rahoto cewa gwamnatin jihar Kogi ta tuhumi Abdul Rahman Ado Ibrahim, Ohinoyi na kasar Ebira, kan zargin kin zuwansa wajen maraba da Shugaba Buhari yayin ziyarar da ya kai jihar.

Kara karanta wannan

Kotun Koli: Babban Mai Adawa Da Buhari Ya Taya Tinubu Murna, Ya Aika Gagarumin Sako Ga Atiku

Buhari ya ziyarci jihar a ranar 29 ga watan Disamban 2022 domin kaddamar da wasu kammalallun ayyuka.

A wasikar tuhumar da Enimola Eniola, daraktan al'amuran masarautu na jihar yasa hannu, yace kin zuwan basaraken wurin tarbar Buhari da gangan ne kuma hakan na iya kawo rikici a jihar Kogi da kasar Ebira.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng