Ba a Aike Min da Gayyata Kan Zuwan Buhari ba, Sarkin Ebira Yayi wa Yahaya Bello Martani

Ba a Aike Min da Gayyata Kan Zuwan Buhari ba, Sarkin Ebira Yayi wa Yahaya Bello Martani

  • Ohinoyin kasar Ibira, Abdulrahman Ado Ibrahim, yayi martani game da wasikar tuhumar da Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya aika masa da ita
  • A wasikar, an zargi basaraken da raini gami da rashin da'a ga gwamnan jihar, bisa kin tarbar shugaban kasa Muhammadu Buhari yayin kai ziyararsa jihar
  • Sai dai, basaraken ya musanta tuhumar gami da bayyana yadda aka bar shi a duhu game da ziyarar, kuma ba a masa adalci ba idan aka zargesa da laifukan

Kogi - Abdulrahman Ado Ibrahim, Ohinoyin kasar Ibira, yayi martani game da takardar tuhumar da gwamnatin jihar Kogi ta tura masa bisa rashin tarbar shugaban kasa Muhammadu Buhari a yayin da ya kai ziyara jihar.

Ohinoyi da Bello
Ba a Aike Min da Gayyata Kan Zuwan Buhari ba, Sarkin Ebira Yayi wa Yahaya Bello Martani. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Basaraken ya bayyana yadda "aka barsa a duhu game da shirye-shiryen tarbar" shugaban kasar, amma ba da gangan ya ki halartar taron ba.

Kara karanta wannan

Bishop Kukah Ya Magantu, Ya Fadi Abun da Babban Hadimin Buhari Ya Fada Masa Bayan Ya Caccaki Fadar Shugaban Kasa

Buhari ya ziyarci Kogi a ranar 29 ga watan Disamba don kaddamar da wasu ayyuka da aka kammala.

Ohinoyin kasar Ibira bai halarci taron tarbar shugaban ba, wanda yasa Enimola Enia, daraktan sarakuna na jihar turo da wasika, inda yake zargin basaraken da gangancin kokarin jefa Kogi cikin "babban rikici."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wasikar ta ce basaraken gargajiyar ya nuna raini da rashin biyayya ga ofishin gwamna, inda ya kara da cewa dole ne ya samar da bayani cikin awanni 48 don me ba za a dauki mataki a kansa ba.

Basaraken yayi martani

Yayin martani ga wasikar tuhumar, a wata wasika da ta fita ranar 6 ga watan Janairu, basaraken gargajiyar ya bayyana yadda bai samu wata takarda da ke bayyana masa cewa Buhari zai ziyarci jihar ba.

"Babu wata takarda da aka aiko da ke sanar min game da ziyarar mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari, game da ziyararsa a ranar 29 ga watan Disamba, 2022, don kaddamar da wasu ayyuka da mai girma Alh. Yahaya Bello, gwmanan jihar Kogi ya jagoranta."

Kara karanta wannan

Buhari Ya Bayyana Ainihin Manufar Ƙirƙirar Ƙungiyar Boko Haram

- A cewar basaraken.

"Sai dai kawai a daren 28 na watan Disamba, 2022, da ka ziyarce ni misalin karfe 9:30 na dare, ka sanar da ni cewa shugaban kasa zai zo Okene washe gari don kaddamar da wasu ayyuka, na zauna a fada ta yayin da shugaban zai karaso ya kawo min ziyara idan ya iso.
"A 29 ga watan Disamba, 2022 misalin karfe 8:15 na safe, wata kwafin abubuwan da za a gudanar a ziyarar shugaban kasa, wacce ban san daga ina ta fito ba ta riske ni, a nan ne na gane shugaban kasa zai kaddamar da fadar Ohinoyi da karfe 10:10 na safe.
"Hakan na nufin shugaban kasa zai kaddamar da wata fada daban da tawa da nake cikin tun daga lokacin da aka nada ni sarauta a 1997.
"Yana da kyau a san cewa, a matsayina na Sarkin kasar Ibira, babu wanda ya sanar da ni game da wata sabuwar fada. Saboda haka ne na shirya tare da bin dokarku in tarbi shugaban kasa kamar yadda al'adarmu ta tsara.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Ce Ya Cika Alkawuran da Ya Dauka, Tinubu Ya Ce ba Haka Abin Yake ba

"Hakan yasa na shirya taro don don nuna masa yabawa da ziyartarsa ta biyu ga Okene tun 1985, da mai martaba marigayi Ohinoyin Ibira, Alh. Sanni Omolori ya tarbesa.
"Nasa an yi kwafin katon hoton ziyarar kusa da kujerar da na samar yayin ziyarar kamar yadda na hada."

Ranar na kai ziyara ga wadanda bom ya tashi dasu, Basarake

Jaridar TheCable ta rahoto cewa, a ranar da Buhari ya kai ziyara, wani abu mai fashewa ya tashi a wani masallaci kusa da fadar Ohinoyi.

Leadership ta rahoto cewa, ya siffata zargin rashin yin biyayyan a matsayin "rashin adalci ga irin gogewarsA da kuna shekarun da Yayi kan karagar mulki, kima da darajarsa."

Ya kara da bayyana yadda yana gab da shirin tarbar shugaban kasar, wani abu mai fashewa ya tashi kusa da fadarsa, wanda hakan yasa na garzaya wajen, yayin da yake tsaka da tabbatar da an kula da wadanda lamarin ya auku dasu, aka sanar dasgi cewa Buhari ya kammala taron kuma ya kama hanyar Lokoja.

Kara karanta wannan

Na Cika Alkawaran Da Na Yiwa Yan Najeriya: Buhari Ya Bayyana Shirinsa Na Gaba Bayan Zaben 2023

"A nan ne na gano an toshe kofar shige da ficen fadata saboda lamarin.
"An barni a duhu game da shirye-shiryen tarbar shugaban kasar da abubuwan da suka dace don tarbar Buhari a Okene, da kuma irin dokin da mutane na su ka yi don tarbarsa."

- Yace.

Gwamna yana barazana ga basarake kan kin zuwa tarbar Buhari

A wani labari na daban, Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya zargi Ohinoyi na kasar Ibira da raini tare da rashin da'a saboda kin zuwa tarbar Buhari a ziyarar da ya kai jihar don kaddamar da waus manyan ayyuka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel