Kungiyar Musulmi Ta Dauki Matakin Ladabtar da Malaman Addini da Ke Kawo Bidi'a, Sun Bayyana Tsari
- Al'ummar Musulmi a jihar Oyo sun kafa kwamitin da zai ladabtar da malamai ma su kawo bidi'a cikin addini
- Kungiyar ta kafa kwamitin ne don tabbatar da bibiyar malaman yayin gudanar da lamuransu don kaucewa kawo sabon abu
- Wannan mataki na zuwa ne bayan kama wani korarren limami kan zargin daddatsa wani don yin tsafi
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Oyo - A kokarin dakile kawo bidi'a a cikin addinin Musulunci, al'ummar Musulmai a jihar Oyo sun shirya daukar mataki.
Majalisar Musulmi a jihar ta kafa sabon kwamitin da zai rika ladabtar da duk wani malamin addini da aka samu sa kawo bidi'a.
Meye dalilin daukar wannan mataki kan malaman a Oyo?
Wannan na cikin wata sanarwa da aka fitar wanda ta ce babban limamin masallacin birnin Ibadan, Sheikh Abdulganiyu Abubakar shi zai jagoranci kwamitin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abdulganiyu har ila yau, shi ne shugaban limaman jihar Oyo, kamar yadda Tribune ta tattaro.
Musabbabin daukar wannan mataki shi ne bayan kama wani malami da jami'an tsaro su ka yi kan zargin daddatsa wani don yin tsafi.
Wanda ake zargin, an kore shi daga limancin babban masallacin wani kauye da ake kira Awotan, cewar Aminiya.
Meye martanin shugaban kungiyar kan malaman a Oyo?
A jawabinsa, shugaban majalisar al'ummar Musulmi a jihar, Alhaji Ishaq Kunle ya ce za su ci gaba da biyar lamuran korarren limamin har zuwa lokacin yanke hukunci.
Ya bayyana cewa kwamitin zai yi aiki tukuru don binciken malamai musamman ma su kawo abubuwa da su ka sabawa koyarwar Musulunci.
Alhaji Kunle ya shawarci mutane da su kai karar duk wani malami da su ke zargin ya na aikata wani abu ga jami'an tsaro.
'Yan sanda sun cafke malaman addini 3 kan fille kan wani
A wani labarin, rundunar 'yan sanda a jihar Oyo ta kama wasu malaman addinin Musulunci uku kan zargin fille kan wani don yin tsafi.
Rundunar ta ce wadanda ake zargin sun yaudari marigayin ne da nufin za su ba shi aikin yi a cikin wani kango a kauyen Awotan.
Jami'an 'yan sandan su ka ce an tsare wadanda ake zargin ne a bangaren binciken manyan laifuka na CID da ke birnin Ibadan.
Asali: Legit.ng