Jerin Kwalejojin Ilimi da Fasaha Na Gwamnati Da Aka Kara Wa Daraja Zuwa Jami'o'i
2 - tsawon mintuna
- Gwamnatin Tarayya da na jihohi sun sauya wasu Kwalejojin Ilimi da Fasahwa zuwa jami'o'i
- An dauki matakin ne domin bai wa karin mutane damar samun ilimin jami'a a cewar tsohon shugaban NUC, Farfesa Abubakar Rasheed
- Sai dai, shugaban kungiyar ASUP na kasa yana yi wa wannan karin darajar kallon wani abu da ka iya kawo cikas ga ilimin kwalejojin fasaha a kasar
Ma'aikacin jaridar Legit Hausa Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe
Gwamnatin Tarayya da na Jihohi sun sauya wasu kwalejojin ilimi da na fasaha zuwa jami'o'i a yayin da ake cigaba da nuna banbanci tsakanin wadanda suka kammala karatu a manyan makarantu.
Wannan rahoton ya tattaro wasu kwalejojin ilimi da kwalejojin fasaha wadanda aka kara wa daraja zuwa jami'o'i.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwalejojin Ilimi da aka sauya su zuwa jami'o'i
- Kwalejin Ilimi na Adeyemi
- Kwalejin Ilimi na Alvan Ikoku
- Kwalejin Ilimi na Saadatu Rimi, Kano
- Kwalejin Ilimi na Emmanuel Ayande
- Kwalejin Ilimi ta Jihar Osun, Ilesha
- Kwalejin Ilimi ta Adeniran Ogunsanya
- Kwalejin Ilimi ta Micheal Otedola
- Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari, Sokoto
- Kwalejin Ilimi ta Agbor
- Kwalejin Ilimi ta Jihar Abiya
Kwalejojin Fasaha ta aka mayar da su jami'o'i
- Kwalejojin Fasaha na jihar Legas
- Kwalejojin Fasaha na jihar Delta, Ozoro
- Kwalejojin Fasaha na Abiya
- Kwalejin Kimiyyar Lafiya da Nazarin Gudanarwa na Jihar Abiya
- Kwalejojin Fasaha na Tarayya, Ilaro
- Kwalejojin Fasaha na Tarayya, Ofa
- Kwalejojin Fasaha na Yaba
- Kwalejojin Fasaha na Kaduna
Asali: Legit.ng