Bayan shekaru 6 suna horo, an yaye dalibai 260 a jami'ar Soji ta NDA

Bayan shekaru 6 suna horo, an yaye dalibai 260 a jami'ar Soji ta NDA

  • An gudanar da bikin yaye daliban makarantar Soji NDA yau a Kaduna
  • Shugaba Buhari ne babban bako na musamman a bikin Faretin
  • Dukkan manyan hafsoshin Najeriya sun halarci bikin mai armashin gaske

Kaduna - Bayan shekaru shida na karatu da horo, jami'ar Sojojin Najeriya (NDA) dake jihar Kaduna ta yaye daliban kas ta 68 su guda Dari biyu da sittin ranar Asabar, 9 ga Oktoba, 2021.

Daliban da aka yaye sun hada da sabbin Sojojin kasa, Mayakan Sama, da Sojojin ruwa, rahoton ChannelsTV.

An yi bikin Faretin ne a hedkwatar NDA dake jihar Kaduna.

Shugaba Muhammadu Buhari ne babban bako na musamman a bikin.

Wadanda ke hallare a taron sun hada da Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, wanda shine masaukin baki da kuma iyaye, 'yan uwa da abokan arzikin daliban da aka yaye.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya dira jihar Kaduna don halartan bikin yaye daliban makarantar Soji NDA

Hakazalika manyan hafsohin Sojin Najeriya fari da Janar Lucky Irabor; babban hafsan Sojin kasa, Laftanan Janar Farouq Yahaya; Babban hafsan sojin sama, Air Marshall Isiaka Amao, da kuma Vice Admiral Awwal Gambo na hallare.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yaushe aka kafa NDA kuma dalibai nawa ta yaye kawo yanzu

An kafa NDA ne a shekarar 1964 domin horar da jami'an Sojojin Najeriya.

Tun bayan kafa kungiyar, makarantar ta yaye dalibai 19,000, cikinsu akwai sojojin kasashen waje.

Bayan shekaru 6 suna horo, an yaye dalibai 260 a jami'ar Soji ta NDA
Bayan shekaru 6 suna horo, an yaye dalibai 260 a jami'ar Soji ta NDA Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Rundunar soji ta kai farmaki sansanin ‘yan bindiga, ta ceto babban sojan da aka sace a NDA

Zaku tuna cewa kwanakin baya yan bindiga sun kai hari makarantar Soji NDA inda suka kashe Soji kuma sukayi garkuwa da Manjo guda.

Manjo CL Datong, wanda aka yi garkuwa da shi lokacin da 'yan bindiga suka kutsa NDA a Kaduna, a watan da ya gabata, ya samu kubuta.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Sojoji sun sako shahararren jarumin Nollywood da suka damke

An kashe manyan jami’an biyu a lamarin wanda ya faru a ranar 24 ga Agusta, 2021.

A daren Juma'a, 17 ga watan Satumba, Mataimakin Daraktan Hulda da Jama'a na Runduna ta 1, Sojojin Najeriya, Kanal Ezindu Idimah, ya ce sojoji sun ceto Datong, jaridar Punch ta ruwaito.

Ya ce ayyukan da suka kai ga kubutar da shi sun kai ga rusa sansanonin ‘yan ta’adda da aka gano a yankunan Afaka- Birnin Gwari na jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Online view pixel