Bayan Dogon Zama, Kotun Zabe Ta Raba Gardama Tsakanin Binani da Fintiri a Adamawa
- An bayyana wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Adamawa bayan kai ruwa rana a kotun kararrakin zabe
- An yi kuskuren alanta Aisha Dahiru Binani a matsayin wacce ta lashe zaben gwamnan a zaben watan Maris
- Ana ci gaba da yanke hukuncin raba gardama tsakanin 'yan takara a jihohi daban-daban a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Jihar Adamawa - Kotun zaben gwamnan jihar Adamawa a ranar Asabar 28 ga watan Oktoba ta tabbatar da sake zaben Umaru Fintiri a matsayin zababben gwamnan jihar a zaben gwamnan da aka yi a watan Maris din bana, Channels Tv ta ruwaito.
Bayan zaben gwamnan Adamawa da ya janyo cece-kuce, Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana Fintiri a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar a karo na biyu.
A karshen kai ruwa rana da aka yi kafin sanar da sakamakon zaben a watan Afrilu, Fintiri na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 430,861, inda ya doke Aisha Dahiru Binani ta jam’iyyar APC mai kuri'u 398,738.
Binani ta tafi kotun zabe
Binani da wasu ’yan takara a fadin kasar nan sun kai kara kotun sauraran kararrakin zabe suna neman ta soke nasarar Fintiri tare da bin kadunsu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai, a hukuncin na yau Asabar, an yiwa Aisha Binani barin makauniya ta hanyar alanta Fintiri a matsayin sahihin wanda ya lashe zaben.
Kitimurmura a zaben Adamawa
A baya, kun ji yadda a ranar 15 ga watan Afrilu baturen zabe ya sanar da Binani a matsayin wacce ta lashe zaben Adamawa.
Hakan ya jawo cece-kuce yayin da aka bayyana cewa, an samu kuskure a tattara sakamkon zaben, kana baturen zaben ya yi riga-malam-masallaci.
Daga baya, an dakatar da tattara sakamakon tare da bayyana mataki na gaba, har ta kai ga alanta Fintiri ne ya yi nasara.
Ban yi dana-sanin alanta Binani ba, inji Hudu Ari
A wani labarin , kwamishinan zabe na Adamawa da aka dakatar, Hudu Yunusa-Ari, ya ce bai yi nadamar ayyana Aisha Binani a matsayin wacce ta lashe zaben gwamna na ranar 15 ga watan Afrilun ba a jihar, jaridar The Cable ta rahoto.
Yunusa-Ari ya haddasa cece-kuce bayan ya bayyana Aisha Binani Dahiru ta jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a matsayin wacce ta lashe zabe yayin da ba a kammala tattara sakamako ba.
Asali: Legit.ng