Gwamna Zulum Ya Bayyana Kananan Hukumomin Jihar Borno da Ke Karkashin Ikon Boko Haram

Gwamna Zulum Ya Bayyana Kananan Hukumomin Jihar Borno da Ke Karkashin Ikon Boko Haram

  • Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya yi magana kan halin da ake ciki dangane da tsaro a jihar
  • Gwamnan ya bayyana cewa tsaron jihar ya inganta da kaso 85% cikin 100 saboda jajircewar jami'an tsaro
  • Gwamna Zulum ya yi nuni da cewa a yanzu babu wata ƙaramar hukuma a jihar da ke ƙarƙashin ikon Boko Haram

Jihar Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, a ranar Juma’a, ya ce al’amuran tsaron jiharsa sun inganta da kaso 85% cikin 100, yana mai cewa babu wani yanki da ke ƙarƙashin ikon Boko Haram.

Zulum ya bayyana hakan ne bayan ya fito daga ganawar sirri da ya yi da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, a fadar Aso Rock da ke Abuja, cewar rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Kotun Koli: Babban Malamin Addini Ya Yi Hasashen Abin da Zai Faru Bayan Yanke Hukunci

Gwamna Zulum ya yi magana kan tsaron jihar Borno
Gwamna Zulum ya yi magana kan tsaron jihar Borno Hoto: @GovBorno
Asali: Twitter
"Magana ta gaskiya, babu ɗaya daga cikin ƙananan hukumomi 27 na jihar Borno da ke ƙarƙashin ikon ƴan tada ƙayar baya." A cewarsa.

Rikicin Boko Haram ya yi ɓarna sosai

A cikin shekaru 14 da suka gabata jihar Borno da jihohin Arewa maso Gabas na Adamawa da Yobe sun zama matattarar ayyukan ta'addanci na Boko Haram.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin watan Yunin 2021, hukumar cigaban majalisar ɗinkin duniya ta ƙiyasta aƙalla mutuwar mutum 350,000 daga tashe-tashen hankula da Boko Haram tun shekarar 2009.

An samu cigaba fannin tsaro a Borno

Da aka tambaye shi halin da ake ciki, Zulum ya kada baki ya ce:

"Gaskiya lamarin tsaro ya inganta a jihar Borno da sama da kaso 85% cikin 100. Ayyukan tattalin arziki na cigaba da tafiya daidai a jihar Borno."
"Na karanta wani rubutu a kwanakin baya na cewa ana samun ƙaruwar ta'addanci a jihar Borno, labarin gaskiya ba ne. Sojojin Najeriya suna ba mu haɗin kan da ake so, ƴan sanda, rundunar sojin sama da sauran sassan rundunar sojin Najeriya suna tallafa mana."

Kara karanta wannan

Tsohon Minista Solomon Dalung Ya Bayyana Mafita 1 Kan Rikice-Rikicen Jihar Plateau

Sai dai, Gwamnan ya ce wasu ƙananan hukumomin da har yanzu ake fama da rikici na tsawon shekaru da dama, mutane ba su gama komawa gaba ɗaya ba.

"Yanzu, an sake tsugunar da mutane a wani bangare, musamman a ƙaramar hukumar Abadam sai kuma ƙaramar hukumar Guzamala." A cewarsa.

Legit Hausa ta samu jin ta baƙin wani mazaunin ƙaramar hukumar Biu a jihar ta Borno, mai suna Malam Aliyu, wanda ya tabbatar da cewa tsaro ya inganta sosai a jihar Borno.

Malam Aliyu ya yi nuni da cewa tsaron da aka samu yanzu ya sanya mutane da yawa sun koma noma yayin da ake cigaba da gudanar da harkokin kasuwanci, a wuraren da a baya ba a iya shiga.

A kalamansa:

"Wannan cigaba ne sosai. A baya mun samu naƙasu a fannin tattalin arziƙi amma yanzu kam Alhamdulillahi, yanayin noma da kasauwanci duk ya dawo wasu wuraren da a da ba a iya shiga a baya yanzu duk ana iya shiga a yi kasuwanci."

Kara karanta wannan

Kotun Koli: Wani Gwamnan PDP Ya Sake Taya Shugaba Tinubu Murna

Zulum Ya Ba Sojoji Tallafi

A wani labarin kuma, gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya raba tallafi ga sojojin da suka samu raunika a wajen yaƙi da ƴan ta'addan Boko Haram.

Gwamna Zulum ya raba Naira miliyan 10 ga sojojin domin rage raɗaɗin raunikan da suka samu yayin fafatawa da ƴan ta'adda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng