'Yan Bindiga Sun Tare Hanya, Sun Halaka Mutum 3 a Jihar Benue
- Miyagun ƴan bindiga ɗauke da makamai sun tare hanya a jihar Benue inda suka salwantar da rayukan mutum uku
- Ƴan bindigan dai sun jera kwanaki biyu suna tare titin babbar hanyar Makurdi-Lafia inda suka aikata aikin ta'addanci
- Ƴan bindigan waɗanɗa suka halaka mutum uku a yayin harin sun kuma raunata wasu mutane da ba su ji ba, ba su gani ba
Jihar Benue - Wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kashe mutum uku a wani harin kwanton ɓauna da suka kai kan hanyar Makurdi-Lafia da ke kewayen Ortese a ƙaramar hukumar Guma ta jihar Benue.
Hakan na zuwa ne kimanin mako guda bayan da ƴan bindiga suka yi wa wasu ƴan gudun hijira uku kwanton ɓauna tare da halaka su, bayan sun je kamun kifi a ƙaramar hukumar Gwer ta Yamma, rahoton Vanguard ya tabbatar.
An tattaro daga wata majiya a yankin cewa maharan da suka yi kwanton ɓauna kan babbar hanyar a ranar Alhamis da yamma da safiyar Juma'a a kusa da ƙauyukan Hirnyam, Pevkyaa da kuma Ortaver sun kuma bar wasu mutane da munanan raunuka.
Yadda harin ya auku
A kalamansa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"A ranar farko wacce ta kasance da yammacin Alhamis, ƴan bindigan sun fito kan hanyar Makurdi-Lafia kusa da gonar NYSC inda suka harbe mutum uku."
"Biyu daga cikin waɗanda aka harba sun mutu nan take amma mutum na uku da ya samu munanan raunuka ya tsira kuma an garzaya da shi asibiti domin yi masa magani."
"Bayan haka, sai suka zo suka sake tare hanyar a safiyar ranar Juma'a, suka harbe wasu mutane. Ɗaya daga cikin waɗanda suka harba ya mutu amma wasu sun tsira."
Menene abinda hukumomi suka ce kan lamarin?
Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, sakataren tsaro na ƙaramar hukumar Guma, Mista Christopher Waku ya ce an kashe mutum uku.
Ya bayyana cewa ƴan bindigan ɗauke da makamai sun yi kwanton ɓauna na kwana biyu a jere a Ortese inda suka harbe mutum uku har lahira a hanyar Daudu/Ortese dake kan babban titin hanyar Makurdi-Lafia.
Da aka tuntubi jami'ar hulɗa da jama'a ta ƴan sandan jihar, SP Catherine Anene ta ce ba ta da masaniya kan lamarin.
Yan Bindiga Sun Halaka Mutane a Kaduna
A wani labarin kuma, ƴan bindiga sun salwantar da rayukan bayin Allah a wani hari da suka kai a ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.
Miyagun ƴan bindigan sun halaka mutum huɗu tare da yin awon gaba da wasu mutanen a harin da suka kai.
Asali: Legit.ng