Jihar Borno: Sarkin Biu Ya Nadawa Tukur Buratai Sarautar Betaran Biu
- Mai martaba Sarkin Biu, Dr Umar Mustapha II, ya bai wa tsohon shugaban hafsan soji, Tukur Buratai sarauta
- An nadawa Buratai sarautar Betaran Biu a ranar Juma'a, 27 ga watan Oktoba, saboda gudunmawar da ya bai wa masarautar ta Biu
- Sarkin ya kuma nada Birgediya Janar Dandan Garba mai ritaya a matsayin Zannan Biu da Rear Admiral Abdul Adamu Biu a matsayin Shattiman Biu
Jihar Borno - Sarkin Biu, Mai martaba Dr Umar Mustapha II, ya nadawa tsohon shugaban hafsan sojin Najeriya, Laftanal Janar Tukur Buratai, sarautar Betaran Biu a ranar Juma'a, 27 ga watan Oktoba.
An nada Zannan Biu da Shattiman Biu
Basaraken mai daraja ta daya ya kuma nada Birgediya Janar Dandan Garba mai ritaya a matsayin Zannan Biu da Rear Admiral Abdul Adamu Biu a matsayin Shattiman Biu.
Zagazola Makama ya rahoto cewa sarki Mustapha ya ce an nadawa manyan jiga-jigan rundunar tsaron sarauta ne saboda gaskiya, amana da jajircewarsu a kan aikin al'ummar jihar da ma Najeriya baki daya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sarkin ya yi bayanin cewa an zabi Buratai ne saboda gudunmawar da ya bai wa masarautar Biu da Najeriya gaba daya.
Mataimakin gwamnan jihar Borno, Dr Usman Kadafur,a ya yaba ma sarkin kan nada masu wadannan sarautu da ya yi da kuma jajircewarsu wajen zaman lafiya da hadin kan Najeriya.
Jerin manyan mutane da suka halarci taron
Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya rahoto cewa taron mai dumbin tarihi wanda ya gudana a fadar sarkin ya samu halartan manyan mutane da yan siyasa, jami'an sojoji masu ci da wadanda suka yi ritaya, manyan gwamnati, sarakunan gargajiya da sauransu.
Wadu daga cikin manyan mutanen da suka hallara sun hada da Shugaban hafsan soji, Laftanal Janar Taoreed Lagbaja; tsohon shugaban hafsan soji, Laftanal Janar Farouk Yahaya; Laftanal Janar Lamidi Adeosun, da tsohon shugaban APC na kasa, Alhaji Abdullahi Adamu.
Ga hotunan bikin nadin a kasa:
Basarake da kotu ta tsige zai daukaka kara
A wani labarin, sansanin Oba Ghandi Afolabi Olaoye, Soun na Ogbomosho wanda wata babbar kotun jihar Oyo ta kora, ya bayyana cewa sarkin zai ɗaukaka ƙara kan hukuncin.
Idan dai za a iya tunawa, a makonnin da suka gabata ne masu zaɓar sarki suka zaɓi Olaoye, wanda fasto ne kuma ɗan kasuwa mai kasuwanci a ƙasashen waje a matsayin sabon Sarkin Ogbomosho wanda ake kira da Soun.
Asali: Legit.ng