Yanzu Yanzu: Shugaban Kasa Tinubu Ya Yi Manyan Nade-Nade 12 a Hukumar Kula Da Ma’aikatan Tarayya

Yanzu Yanzu: Shugaban Kasa Tinubu Ya Yi Manyan Nade-Nade 12 a Hukumar Kula Da Ma’aikatan Tarayya

  • An samu sauye-sauye a hukumar kula da ma'aikatan tarayya yayin da shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da sabbin nade-nade 12
  • Tinubu ya nada sabon shugaba da mambobin hukumar FCSC a ranar Juma'a, 27 ga watan Oktoba
  • Shugaban kasar ya bukaci majalisar dattawa da ta tantance tare da tabbatar da mutanen da aka zaba a wannan mukamai

Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada sabon shugaba da mambobin hukumar kula da ma'aikatan gwamnatin tarayya (FCSC).

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara ta musamman kan harkokin labarai, Ajuri Ngelale, ya saki a ranar Juma'a, 27 ga watan Oktoba.

Tinubu ya yi nade-nade a hukumar FCSC
Yanzu Yanzu: Shugaban Kasa Tinubu Ya Yi Manyan Nade-Nade 12 a Hukumar Kula Da Ma’aikatan Tarayya Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Ngelale ya bayyana cewa shugaban kasar ya yi nadin ne bisa karfin ikon da sashi na 154 na kundin tsarin mulkin Najeriya (kamar yadda aka gyara) ya ba shi.

Kara karanta wannan

Jiga-jigan PDP 4 da Su ka Nuna Farin Ciki da Nasarar Tinubu Kan Atiku a Kotun Koli

Ya kuma bayyana cewa ana jiran majalisar dattawa ta tantance tare da tabbatar da wadanda aka nada kan mukaman.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sunayen wadanda Tinubu ya nada a hukumar FCSC

  1. Farfesa Tunji Olaopa — Shugaba
  2. Dr. Daudu Ibrahim Jalo — Mamba (Zai wakilci Adamawa | Gombe | Taraba)
  3. Ms. Gekpe Grace Isu — Mamba (Za ta wakilci Akwa Ibom | Cross River)
  4. Dr. Chamberlain Nwele — Mamba (Zai wakilci Anambra | Ebonyi | Enugu)
  5. Mista Rufus N. Godwins — Mamba (Zai wakilci Rivers | Delta | Bayelsa)
  6. Dr. Adamu Hussein — Mamba (Zai wakilci Niger | Babban birnin tarayya)
  7. Mista Aminu Nabegu — Mamba (Zai wakilci Jigawa | Kano)
  8. Ms. Hindatu Abdullahi — Mamba (Za ta wakilci Kaduna | Katsina)
  9. Mista Shehu Aliyu — Mamba (Zai wakilci Kebbi | Sokoto | Zamfara)
  10. Ms. Odekunle Rukiyat Aduke — Mamba (Za ta wakilci Kogi | Kwara)
  11. Mista Jide Jimoh — Mamba (Zai wakilci Lagos | Ogun)
  12. Dr. Festus Oyebade — Mamba (Zai wakilci Osun | Oyo)

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Tinubu Ya Kori Daraktocin Hukumar NIWA, NSC Ya Maye Gurbinsu

Tinubu ya yi nade-nade a ma'aikatar lafiya

A wani labari makamancin wannan, Legit Hausa ta rahoto a baya cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da nadin sabbin shugabanni biyu domin jagorantar hukumomi a ma'aikatar kiwon lafiya.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara ta musamman kan harkokin labarai, Ajuri Ngelale, ya saki a ranar Juma'a, 20 ga watan Oktoba.

Sabbin shugabannin da aka nada sune Dr Muyi Aina, shugaban hukumar kula da lafiya a matakin farko ta kasa (NPHCDA) da Dr Kelechi Ohiri, shugaban hukumar inshorar lafiya ta kasa (NHIA).

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng