Katsina: Ba Zamu Nemi Tattauna Wa da Yan Bindiga Ba, Malam Dikko Radda

Katsina: Ba Zamu Nemi Tattauna Wa da Yan Bindiga Ba, Malam Dikko Radda

  • Malam Dikko Radda ya jaddada cewa gwamnatinaa ta ba zata tattauna da 'yan bindiga da sunan tana neman sulhu ba
  • Ya ce zai yi amfani da isasshen ƙarfin soji wajen magance matsalar tsaro har sai yan ta'adda sun kawo kansu teburin sulhu
  • Babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya ya yaba wa gwamnan bisa kirkiro da dakarun 'yan sa'kai da zasu taimaka wa jami'an tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗda, ya ce gwamnatinsa ba zata nemi tattaunawar sulhu da 'yan bindiga ba ta ko wace hanya.

Amma a maimakon haka Gwamnan ya kuduri aniyar yin amfani da isassun karfin soji don tursasa ‘yan fashin dajin su miƙa wuya, su taho zuwa kan teburin tattaunawa.

Gwamnan Katsina ya ziyarci babban hafsan tsaro a Abuja.
Katsina: Ba Zamu Nemi Tattauna Wa da Yan Bindiga Ba, Malam Dikko Radda Hoto: Isah Miqdad
Asali: Twitter

Malam Raɗɗa ya yi wannan furucin ne yayin da ya ziyarci babban hafsan tsaron Najeriya (CDS), Janar Christopher Musa, a ofishinsa da ke Abuja ranar Alhamis, 26 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Ana Tsaka da Murnar Nasarar Tinubu, Babban Jigon APC Ya Rasu a Hatsarin Jirgi a Bayelsa

Isah Miqdad, babban mai taimakawa gwamnan kan harkokin midiya ne ya tabbatar da haka a shafinsa na Manhajar X watau Tuwita.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A jawabinsa gwamna Raɗda ya ce:

"Tsohuwar gwamnatin da ta wuce ta rungumi tattaumawa da yan bindigan daji amma hakan bai haifar da ɗa mai ido ba, zamu yi amfani da karfi wajen magance wannan matsala ta tsaro."
"A yanzu ba zamu tattauna da yan bindiga don su amfana ba, muna son zama teburin sulhu ne idan suka ji ba sauƙi sai Allah suka fito da kansu suka ce sun shirya tattaunawa."
"A wannan lokacin ne zamu iya saurarensu, kana mu san yadda za ai mu gyara musu ɗabi'u su koma rayuwa a cikin al'umma."

Abin da ya sa na kafa rundunar tsaro - Radda

Gwamnan ya ce ya kaddamar da rundunar tsaro ta al’umma a jihar ne domin kara karfafa kokarin sojoji da sauran jami’an tsaro a yakin da ake yi da ‘yan bindiga.

Kara karanta wannan

Gwamna Uba Sani Ya Gana da Shugaba Tinubu a Villa Kan Muhimman Abu 3, Ya Yi Bayani

Ya ce ya ziyarci hedikwatar tsaro ne domin karfafa alakar da ke tsakanin jihar Katsina da rundunar sojin Najeriya.

Radɗa ya yabawa sojoji bisa rawar da suke takawa wajen tabbatar da tsaro a jihar da ma fadin kasar nan.

CDS ya yaba wa gwamna Raɗda

A nasa jawabin, babban hafsan hafsoshin tsaron ya godewa gwamnan bisa wannan shiri na jami’an tsaro na al’umma, ya kuma yi kira ga sauran gwamnonin da su yi koyi da shi ta wannan fanni.

Ya shawarci gwamnonin jihohin Arewa maso Yamma da su hada kai kan yadda za a rage matsalolin tsaro da suka addabi shiyyar.

'Yan bindiga sama da 100 sun baƙunci lahira

A wani rahoton na daban Sojin saman Najeriya sun halaka 'yan bindiga sama da 100 a wani ruwan bama-bamai da suka yi a iyakar jihohin arewa biyu.

Hedkwatar tsaro ta ƙasa DHQ ta bayyana cewa a cikin mako ɗaya, sojoji sun aika gomman da yan bindiga lahira, sun damƙe wasu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262