Fusatattun Matasa Sun Hallaka Wani Mutum Kan Zargin Satar Mazakuta a Abuja

Fusatattun Matasa Sun Hallaka Wani Mutum Kan Zargin Satar Mazakuta a Abuja

  • Wasu fusatattun matasa sun yi ajalin wani Alhaji Tijjani Yakubu kan zargin satar mazakuta a birnin Abuja a jiya Laraba
  • Wanda ya ke ikirarin an sace masa mazakutar mai suna Emmanuel Danladi an garzaya da shi asibiti inda aka tabbatar ta na nan
  • Kwamishinan ‘yan sanda a birnin, Haruna Garba ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya gargadi mutane su guji daukar doka a hannu

FCT, Abuja – Rundunar ‘yan sanda a birnin Tarayya Abuja ta tabbatar da mutuwar wani da ake zargi da satar mazakuta.

Wasu fusatattun matasa ne su ka hallaka mutumin mai suna Alhaji Tijjani Yakubu kan zargin sace wa Emmanuel Danladi mazakuta a kauyen Kabusa da ke Abuja.

Wasu matasa sun yi ajalin mutumi kan zargin satar mazakuta
Matasa Sun Yi Ajlin Wani Kan Zargin Satar Mazakuta a Abuja. Hoto: NPF.
Asali: Facebook

Meye 'yan sanda su ka ce kan satar mazakuta?

Kwamishinan ‘yan sanda a birnin, Haruna Garba shi ya tabbatar da haka yayin ganawa da ‘yan jaridu a jiya Laraba 25 ga watan Oktoba, Daily Trust ta tattaro.

Kara karanta wannan

Legas: Mutane 18 Sun Ga Ikon Allah Yayin da Wani Mummunan Hatsarin Mota Ya Rutsa da Su, Sun Sha Da Ƙyar

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haruna ya ce bayan samun rahoton jami’ansu sun kamo wanda ake zargi da kisan kan zargin satar mazakuta.

Ya ce daga baya an dauki wanda aka lakadawa dukan zuwa asibiti amma zuwansu ke da wuya likita ya tabbatar da mutuwar Alhaji Tijjani, cewar Linda Ikeji.

Ya kara da cewa an kai Emmanuel asibiti don bincikar mazakutar ta shi inda aka tabbatar babu abin da ya same ta.

Wane gargadi 'yan sanda su ka yi kan satar mazakuta?

A cewarsa:

“Mun dauki wanda aka yi wa dukan zuwa asibiti amma isar mu ke da wuya likita ya sanar da mutuwar Tijjani, har ila yau, likitan ya tabbatar da cewa mazakutar Emmanuel tana nan ba abin da ya same ta.”

Ya tabbatar da cewa Emmanuel da wasu mutane biyu da ake zargi su na hannunsu inda ya ce su na kammala bincike za su gurfanar da su a gaban kotu.

Kara karanta wannan

Birnin Gwari: An Kuma Rasa Mutane da ‘Yan Bindiga Su Ka Kai Hare-Hare a Kaduna

Kwamishinan ya ce abubuawa da dama makamancin wadannan na yawan faruwa a birnin inda ya ce a kwanakinna sun kwaci wani mai suna Mathew Michael daga hannun wasu da ke kokarin kashe shi.

‘Yan sanda sun kama mutane 14 kan karyar satar mazakuta

A wani labarin, ‘yan sanda sun kama wasu mutane 14 kan karairayin satar mazakuta a Abuja.

Rundunar ta gargadi mutane da su guji yada jita-jita da daukar doka a hannu musamman kan irin haka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.