Dakarun Sojoji Sun Murkushe Mayakan Boko Haram 5 a Jihar Yobe
- Dakarun Operation Lafiya Dole sun yi gagarumin nasara kan yan ta’addan Boko Haram a jihar Yobe
- Sojoji sun murkushe mayakan kungiyar ta’addanci biyar a garin Geidam da ke karamar hukumar Geidam sun kuma kama daya
- Jama’ar gari sun cika da murna domin yan ta’addan sun addabe su da hare-hare a yan baya-bayan nan
Jihar Yobe - Jama'a sun cika da farin ciki a garin Geidam da ke karamar hukumar Geidam ta jihar Yobe bayan dakarun rundunar sojojin Najeriya sun halaka mayakan kungiyar ta'addanci guda biyar tare da kama wani daya a daren ranar Laraba, 25 ga watan Oktoba.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an kwato bindigogin AK-47 da dama da babura mallakin yan ta'addan a yayin faruwar lamarin inda sauran yan ta'addan suka tsere da raunuka da suka samu sanadiyar harbi.
Al'ummar Geidam na murnar kashe mayakan Boko Haram
Wani dan kasuwa a yankin da ya nemi a sakaya sunansa, ya fada ma Daily Trust cewa mazauna yankin sun cika da fari ciki kan wannan ci gaban, cewa ayyukan Boko Haram a wajen Geidam ya karu a yan baya-bayan nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce:
“Muna farin ciki da matakin gaggawa da dakarun rundunar sojoji suka dauka a nan Geidam ta hanyar kashe yan Boko Haram biyar. Wannan ci gaban na zuwa ne a daidai lokacin da manoma da dama ke tsoron zuwa gonaki sakamakon hauhawan hare-harensu.
"A watanni biyu da suka gabata, sun kashe jami'an tsaro fiye da 3 sannan sun yi barazana ga manoma. Mutane na ta korafin cewa jami'an tsaro basa yin abun da ya dace don magance matsalar don haka sojoji basu ji dadin haka ba wanda shine dalilin da yasa dakarun Operatin Lafiya Dole suka yi kokarin rage hare-haren."
Jam'iyyar APC Ta Yi Martani Bayan INEC Ta Cire Sunan Dan Takararta a Cikin Jerin Yan Takarar Gwamnan Bayelsa
A ranar Asabar da ta gabata ne yan ta'adda suka farmaki gidan Kwastam a garin Geidam, inda suka kashe jami'i daya mai suna Usman Gombe.
Wani jigo a garin Geidam, Ambassador Khalid Geidam, ya ce sojojin sun yi artabu da yan ta'addan bayan samun bayanai abun dogaro game da ayyukan Boko Haram a kusa da Jororo.
Ya ce:
"Dakarun Bataliya ta 159 Geidam karkashin jagorancin kwamandansu sun farmaki mabuyar Boko Harama a Jororo sannan suka kashe yan ta'adda biyar da kama daya, sannan sun samo bindigogin AK-47 da dama yayin da sauran suka tsere da raunin bindiga."
Sojoji sun sheke yan ta'adda a Sokoto
A wani labarin, mun ji cewa dakarun sojoji sun sheke ƴan ta’adda da dama tare da nasarar kwato makamai a jihar Sokoto.
Daraktan hulɗa da jama'a na rundunar, Birgediya-Janar Onyema Nwachukwu, ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar.
Asali: Legit.ng