Alkalan Kotun Koli 7 da Za Su Yanke Hukunci Kan Kararrakin Atiku da Peter Obi
FCT, Abuja - Taƙaddamar shari'a tsakanin ƴan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar da Peter Obi na jam'iyyar Labour da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC zai zo ƙarshe a ranar Alhamis 26 ga watan Oktoba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Kotun ƙoli za ta yanke hukuncin ƙarshe kan ƙararrakin da Atiku da Obi suka shigar inda suke ƙalubalantar hukuncin kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa (PEPC) da ta tabbatar da nasarar Tinubu.
Alƙalan kotun ƙoli bakwai ne za su yanke hukunci kan makomar Atiku, Obi da Tinubu.
A cewar jaridar The Nation, ga cikakkun bayanai kan alƙalan kotun ƙoli guda bakwai da za su zartar da hukunci:
1. Mai shari'a John Inyang Okoro
Mai shari'a Okoro, wanda a halin yanzu shi ne alƙali na huɗu mafi girma a kotun ƙoli, zai jagoranci ƙararrakin da Atiku da Obi suka shigar a kan Tinubu a ranar Alhamis 26 ga watan Oktoba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya zama lauyan Najeriya a 1985 kuma ya zama alƙalin kotun ƙoli a ranar 15 ga watan Nuwamban 2013.
Ya fito daga Nung Ukim, a ƙaramar hukumar Ikono ta jihar Akwa Ibom.
Mai shari'a Okoro ya halarci makarantar koyon aikin lauya ta Najeriya da ke Legas
2. Mai shari'a Uwani Musa Abba-Aji
Mai shari'a Abba Aji, wacce aka haifa a ranar 7 ga Nuwamba, 1956, a Gashua, jihar Yobe, ita ce mace tilo da ta kasance mai shari'a daga cikin alƙalan kotun guda bakwai.
Mai shari'a Uwani, wacce ita ce mace mafi girma a kotun ƙoli ta zama lauya a shekarar 1981.
Ta fara aikinta na shari'a ne a matsayin lauyan gwamnati a shekarar 1982 kuma ta zama mai shari'a mace ta farko a fannin shari'a a jihar Yobe a shekarar 1991, kamar yadda shafin yanar gizon kotun ƙoli ya bayyana.
Jigon PDP Ya Bayyana Dalilin da Ya Kamata Ya Sa Kotun Koli Ta Kori Tinubu Ta Ayyana Atiku Shugaban kasa
Mai shari’a Abba-Aji ta bar mukaminta na alƙalin babbar kotu bayan ta samu ƙarin girma zuwa kotun ɗaukaka ƙara sannan daga bisani ta koma kotun ƙoli a ranar 8 ga watan Janairun 2019.
3. Mai shari'a Ibrahim Saulawa
Mai shari'a Saulawa ya zama lauya a ranar 2 ga Yulin 1982, kuma ya samu ƙarin girma zuwa kotun ƙoli a ranar 10 ga watan Nuwamban 2020.
Kafin ya zama alƙalin kotun ƙoli, mai shari'a Saulawa ya samu ƙarin girma zuwa kotun ɗaukaka ƙara a ranar 10 ga watan Yunin 2006.
Mai shari'a Saulawa wanda ɗan asalin jihar Katsina ne, an haife shi a ranar 29 ga watan Satumban 1956.
4. Mai shari'a Mohammed Lawal Garba
Mai shari’a Mohammed Lawal Garba shi ne shugaban alƙalan kotun zaɓen shugaban ƙasa da ta yi watsi da ƙarar da Atiku ya shigar na ƙalubalantar nasarar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, a 2019.
Ya kuma kasance mamba a kotun zaben shugaban ƙasa a shekarar 2011. Ya samu ƙarin girma zuwa kotun kotun ƙoli a ranar 6 ga watan Nuwamban 2020.
Garba wanda ɗan asalin jihar Zamfara ne ya zama lauya a shekarar 1981 kuma ya zama alƙalin babbar kotun shari'a ta jihar Sokoto daga 1993 zuwa 1996.
Mai shari'a Garba, wanda aka haifa a ranar 16 ga watan Nuwamban 1958, ya kuma riƙe muƙamin babban alƙalin babbar kotun shari'a ta jihar Zamfara daga 1996 zuwa 2004.
5. Mai shari'a Tijjani Abubakar
Mai shari’a Tijjani Abubakar ya samu ƙarin girma zuwa kotun ƙoli a shekarar 2020 yayin da yake aiki a kotun ɗaukaka ƙara da ke Legas.
Tijjani wanda ya fito daga jihar Yobe an haife shi ne a ranar 15 ga watan Afrilun 1960, kuma ya zama lauya a shekarar 1983.
6. Mai shari'a Adamu Jauro
Mai shari'a Adamu Jauro ya yi digirinsa na farko a fannin shari'a a shekarar 1980 a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya a jihar Kaduna.
An haifi Jauro a ranar 26 ga watan Yunin 1959, a jihar Gombe. Ya samu ƙarin girma zuwa kotun ƙoli a watan Nuwamban 2020 bayan ya yi aiki a kotun daukaka ƙara tun shekarar 2007.
Jauro ya zama lauya a shekarar 1983 kuma nan da nan ya fara aiki a ma'aikatar shari'a.
7. Mai shari'a Emmanuel Agim
Mai shari'a Emmanuel Agim ya kasance tsohon alƙalin alƙalan Gambia daga 2009 zuwa 2013 kuma tsohon alƙalin alƙalan ƙasar Swaziland.
Mai shari’a Agim, wanda aka haifa a ranar 26 ga watan Afrilun 1960, a garin Obudu, jihar Cross Rivers, tsohon mai shari'a ne a kotun ɗaukaka ƙara.
Ya yi digirinsa na farko a fannin shari'a a jami'ar Calabar LLB (Hons) sannan ya halarci makarantar shari'a ta Najeriya a Legas
Justice Agim kuma yana samu kwalin LLM daga jami'ar Wolverhampton da ke UK.
Abubuwan Da Kotun Koli Za Ta Yi Hukunci a Kai
Rahoto ya zo kan abubuwan da kotun ƙoli za ta yanke hukunci a kansu a ƙararrakin da Atiku Abubakar da Peter Obi suka shigar kan nasarar Shugaba Tinubu.
Ƴan takarar na jam'iyyun adawa sun yi zargin an tafka maguɗi da rashin bin ƙa'idojin dokar zaɓe a zaɓen da ya samar da shugaban ƙasa Bola Tinubu.
Asali: Legit.ng