Kungiya Ta Yi Magana Bayan Tinubu Ya Nada Yaron Amininsa a Matsayin Shugaban NADF

Kungiya Ta Yi Magana Bayan Tinubu Ya Nada Yaron Amininsa a Matsayin Shugaban NADF

  • A makon da ya gabata, fadar shugaban kasa ta sanar da nadin Muhammad Abu Ibrahim a matsayin shugaban NADF
  • Masu noman kaji a Katsina sun ce an ajiye kwarya a gurbinta domin matashin ya kware a bangaren da aka kai shi
  • Kafin jagorantar gidauniyar aikin gonan, Muhammad Abu Ibrahim ya yi aikin zamantar da noma d kiwo a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abuja - Nadin da aka yi na Muhammad Abu Ibrahim a matsayin Shugaban gidauniyar NADF ta cigaban aikin gona ya jawo abin yabo.

Kungiyar masu kiwon kaji a Katsina ta ji dadin zabin Bola Ahmed Tinubu wajen nada Shugaban NADF, Daily Trust ta fitar da rahoton a yau.

Nada Muhammad Abu Ibrahim ya jagoranci gidauniyar mataki ne da zai kawo cigaba da wuri a bangaren harkar gona a cewar kungiyar.

Kara karanta wannan

Wuta Ta Kunno a APC, Ana Rikici Tsakanin Minista da Shugaban Majalisar Tarayya

Muhammad Abu Ibrahim
Shugaban kasa ya nada Muhammad Abu Ibrahim Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jagororin masu kiwon kaji na reshen jihar Katsina sun fitar da jawabi na musamman ta bakin shugabansu, Haladu Ashiru Kofar Sauri.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mahaifinsa, Sanata Abu Ibrahim ya na cikin wadanda su ka dade tare da Bola Tinubu.

NADF: Tinubu ya ajiye kwarya a gurbinta

Alhaji Haladu Ashiru Kofar Sauri yake cewa an dauko kwararren Akanta wanda ya yi fice a harkar kula da shugabanci da kuma bangaren fasaha.

Rahoton ya ce shugaban makiyayan ya kara da cewa kafin ba shi mukamin nan, Alhaji Abu Ibrahim ya kware wajen samar da kudin aikin gona.

Inda Shugaban NADF ya yi aiki a baya

Sabon shugaban na NADF ya na cikin wadanda su ka kafa kamfanin Sponge Analytics wanda ya zamantar da harkokin gona a kasar nan.

Kamfanin Sponge Analytics ya hada kai da MTN wajen kawowa manoma mafita, bayan nan kuma ya kafa Livestock247 domin masu kiwo.

Kara karanta wannan

ICPC: Jerin Mutum 8 da Su ka Rike Shugabancin Takawarar EFCC a Tsawon Shekara 23

Har ila yau, ya rike shugabanci a kamfanonin noma, fasaha, ilmi da na muhalli.

A karshen jawabin Kofar Sauri, ya yi wa wannan shugaba addu’ar samun damar sauke nauyi, ya ce hakan zai kara karfin gwiwar matasa.

Abu Ibrahim da Tinubu

A lokacin zaben shugaban kasa, an rahoto Abu Ibrahim ya na cewa Bola Tinubu, zai kare muradun mutanen Arewa muddin ya dare kan mulki.

'Dan siyasar ya yi kira ga mutanen Arewacin Najeriya su tuna da Tinubu ya taimakawa na su (Muhammadu Buhari) a zabukan baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng