Gwamna Uba Sani Ya Gana da Shugaba Tinubu, Ya Fadi Abubuwan da Suka Tattauna
- Malam Uba Sani ya gana da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a fadar gwamnatin tarayya da ke Abuja
- Gwamann ya ce sun tattauna muhimman batutuwa da shugaban ƙasa wanda suka shafi jihar Kaduna musamman sha'anin tsaro
- Sani ya yaba wa Bola Tinubu bisa yadda ya ɗauki al'amuran Kaduna da muhimmanci, ya ce ya je Villa ne ya tuna masa
FCT Abuja - Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta kara tsoma hannu tare da tallafa musu a fannonin noma, kiwon lafiya da tsaro.
Uba Sani ya bayyana haka ne yayin hira da masu ɗauko rahoto daga fadar shugaban ƙasa jim kaɗan bayan ya gana da shugaba Bola Ahmed Tinubu ranar Talata.
Sanata Uba Sani ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook da safiyar Laraba.
Ya ce ya ziyarci Tinubu tare da shugaban majalisar wakilan tarayya, Tajudeen Abbas da kuma Dakta Yusuf Hamisu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan ya jadadda muhimmancin haɗa kai da wasu hukumomin gwamnatin tarayya domin kawo karshen ƙalubalen rashin tsaro a faɗin jihar Kaduna.
Me suka tattauna yayin ganawar?
A kalamansa, Gwamna Uba Sani ya ce:
“Na zo nan ne don tattaunawa da Shugaban kasa wanda ke goyon bayan abin da muke yi a Kaduna. Saboda haka na zo bibiya ne kawai kuma na tuna masa wasu ɓangarorin."
Gwamnan ya kuma yabawa shugaban bisa goyon bayan da yake bai wa jihar, inda ya bayyana ganawar da ya yi da Tinubu a matsayin nasara.
“Mun samu shugaban kasa da ya dauki Kaduna da muhimmanci, kuma yana taimaka mana a wuraren da mu jaha ba za mu iya tunkara mu kaɗai ba. Shi ke jagoranta kana ya nuna mana hanya."
Dangane da batun tsaro, Sani ya ce “Muna bukatar karin dakaru a yankuna kamar Birnin Gwari, Giwa da kuma wasu kananan hukumomin da ke kusa da Zangon Kataf, Kaura da kuma wasu sassan Kudancin Kaduna."
"Sojoji sun aminta da cewa Kaduna na daya daga cikin jihohin da ke bukatar tallafin tsaro na gaske saboda kowa ya sani tsaro na hannun gwamnatin tarayya musamman batun hafsoshin tsaro, yan sanda da DSS."
Gwamnoni Huɗu Sun Gana da Gwamnan Ondo
A wani rahoton na daban Gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu, ya karɓi bakuncin gwamnonin Kudu maso Yamma a gidansa da ke Ibadan, jihar Oyo.
Tun bayan dawowa daga jinya a ƙasar Jamus, gwamnan ya tsaya a gidansa na jihar Oyo ba tare da ya koma jihar Ondo ba.
Asali: Legit.ng