Wazirin Fika, Adamu Ya Riga Mu Gidan Gaskiya Ya Na da Shekaru 90
- Ana cikin makoki bayan rasuwar Shahararren dan siyasa kuma ma'aikacin gwamnati, Alhaji Adamu Fika
- Marigayin ya rasu ne a daren jiya Talata 24 ga watan Oktoba yayin da ya ke cikin jirgi a kan hanyar dawo wa Najeriya
- Fika ya rike mukamai da dama da su ka hada Sakataren Gwamnatin Tarayya da shugaban ma'aikatan Gwamnatin Tarayya da sauransu
Jihar Kaduna - Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Adamu Fika ya rasu ya na da shekaru 90 a duniya.
Marigayin wanda shi ne Wazirin Fika ya rasu a daren jiya Talata 24 ga watan Oktoba a cikin jirgi yayin da ake dawo da shi da daga Ingila.
Yaushe marigayin, Wazirin Fika ya rasu?
Danburan Fika, Alhaji Idris Adama Kukuri shi ya tabbatar wa Daily Trust labarin mutuwar a wata ganawa ta wayar tarho.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Har zuwa yanzu ba a sanar da lokacin jana'izar ba inda majiyarmu ta ce sai an tuntubi Sarkin Fika, Alhaji Muhammadu Abali.
Majiyar ta ce jirgin da ya dauko marigayin ya sauka a Kaduna inda ake tunanin binne shi a can ko kuma komawa da shi Fika da ke jihar Yobe.
Wasu mukamin marigayin, Wazirin Fika ya rike?
Fika, kafin rasuwarshi ya rike mukamai da dama a gwamnati da samun lambar yabo masu tarin gaske, Leadership ta tattaro.
Fika kafin rasuwarshi, ya rike mukamin sakataren din-din-din a ma'aikatun Gwamnatin Tarayya da dama da su ka hada da ma'aikatar Kasuwanci da Sadarwa da kuma ta harkokin cikin gida.
Za a yi sallar jana'izarsa a masallacin Sultan Bello da ke birnin Kaduna a yau Laraba 25 ga watan Oktoba dai misalin karfe 4:00 na yamma.
Sabon kwamishina a jihar Borno ya riga mu gidan gaskiya
A wani labarin, sabon kwamishina a jihar Borno, injiniya Ibrahim Idris Garba ya riga mu gidan gaskiya a gidansa da ke Maiduguri babban birnin jihar.
Marigayin ya rasu ne da safiyar ranar Asabar 21 ga watan Oktoba a rukunin gidajen 777 a birnin Maiduguri da ke jihar Borno.
Rasuwar tashi na zuwa ne kwanaki kadan bayan Gwamna Babagana Zulum ya nada shi kwamishinan ayyuka da gyararraki da sake matsuguni a jihar.
Asali: Legit.ng