Yan Bindiga Sun Sace Malamar Jami'a a Jihar Nasarawa
- Ƴan bindiga sun je har cikin gida sun yi awon gaba da wata malamar jami'a a jami'ar jihar Nasarawa da ke Keffi
- Lamarin dai na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan ƴan bindiga sun sace mataimakin shugaban jami'ar da wasu ɗalibai huɗu
- Mazauna ƙaramar hukumar Keffi sun koka kan ƙaruwar hare-haren ƴan bindiga inda suka buƙaci gwamnati da ta kawo musu ɗauki
Jihar Nasarawa - Wasu mahara ɗauke da muggan makamai a daren ranar Lahadi, sun yi awon gaba da wata malamar jami'a ta jami’ar jihar Nasarawa da ke Keffi, Dakta Comfort Adokwe, cewar rahoton Daily Trust.
Jaridar The Punch ta ce ƴan bindigan sun kai farmaki gidanta ne da ke Angwan Jaba a cikin ƙaramar hukumar Keffi, inda suka yi awon gaba da ita yayin da suke ta harbe-harben bindiga.
Lamarin dai na zuwa ne bayan makonni biyu da sace mataimakin shugaban jami'ar da wasu ɗalibai huɗu na jami'ar.
Al'ummar yankin sun koka kan hare-haren yan bindiga
Da yake tofa albarkacin bakinsa kan lamarin a ranar Talata, 24 ga watan Oktoba, wani mazaunin ƙaramar hukumar Keffi, Musa Adamu, ya koka kan yadda ake yin garkuwa da mutane da kuma hare-haren ƴan bindiga a jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Adamu ya buƙaci gwamnatin tarayya da ta ƙara kaimi wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al'umma.
"Sace mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba, ya zama sana'a mai riba ga wasu miyagun mutane. Ya kamata gwamnatocin tarayya da na jihohi su gaggauta shawo kan matsalar domin kwantar da hankulan mutane." A cewarsa.
Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ƴan sandan jihar Nasarawa, Ramhan Nansel, ya ci tura domin bai amsa kiran da aka yi masa ta waya ba har ya zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.
Tsshin Hankali Yayin da Jami'an Tsaro Suka Yi Artabu da Kasurgumin Dan Ta'adda a Babban Birnin Jihar Arewa
Yan Bindiga Sun Gamu da Ajalinsu
A wani labarin kuma, wasu miyagun ƴan bindiga sun gamu da ajalinsu bayan sun je kai harin ramuwar gayya a ƙauyen Tukandu na jihar Sokoto.
Dakarun sojoji sun yi musayar wuta da ƴan bindigan a yayin harin da suka kai inda suka halaka da yawa daga cikinsu, tare da ƙwato makamai da bindigogi masu yawa.
Asali: Legit.ng