Sabon Shugaban EFCC Ya Tilasta Ma'aikantan Hukumar Bayyana Kadarorinsu

Sabon Shugaban EFCC Ya Tilasta Ma'aikantan Hukumar Bayyana Kadarorinsu

  • Sabon shugaban Hukumar EFCC, Ola Olukoyede ya umarci dukkan ma'aikatan hukumar su bayyana kadarorinsu
  • Ola ya ce wannan shi ne tsarin da ake bi a ko ina don haka dole su ma su bi irin tsarin kamar yadda doka ta ambata
  • Ya ce daga mataki na 17 zuwa kasa kowa dole ya bayyana kadarorinsa tun da shi ma a matsayin shugaba ya yi hakan don haka babu wani batun tsoro

FCT, Abuja - Shugaban Hukumar EFCC, Ola Olukoyede ta bukaci dukkan ma'aikatan hukumar su bayyana kadarorinsu.

Ola ya kuma bukaci manyan masu mukamai a hukumar da su ma su bayyana kadarorinsu inda ya ce kada su ji tsoron komai.

Shugaban EFCC ya bukaci dukkan jami'an hukumar su bayyana kadarorinsu
Sabon Shugaban EFCC kawo sabon tsari a hukumar kan ma'akata. Hoto: EFCC.
Asali: Twitter

Meye shugaban EFCC ke cewa?

Shugaban hukumar ya bayyana haka ne a yau Talata 24 ga watan Oktoba a hedkwatar hukumar da ke Abuja.

Kara karanta wannan

ICPC: Jerin Mutum 8 da Su ka Rike Shugabancin Takawarar EFCC a Tsawon Shekara 23

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce dole ne su yi aiki da doka ganin cewa hukumar kanta a karkashin doka ta ke.

A cewarsa:

"EFCC doka ce ta kirkire ta, don haka dole mu bi dokoki yadda ya dace.
"Wannan shi ne abin da ko wace hukumar kasa da kasa ke yi don haka dole mu mayar da shi al'adarmu.
"Dole mu bayyana kadarorinmu daga mataki na 17 zuwa kasa, ni ma na bayyana nawa, don haka babu dalilin da wani zai ji tsoro."

Ya ce hatta sakataren hukumar shi ma ya yi hakan duk da girma ofishinsa, Vanguard ta tattaro.

Wace shawara shugaban EFCC ya bai ma'aikata?

Shugaban ya kara da cewa bayan bayyana kadarorin nasu kuma za su binciki komai da ke tattare da shi, The Nation ta tattaro.

Ya kara da cewa:

Kara karanta wannan

Nyesom Wike Ya Kinkimo Doka, Marasa Biyan Haraji Za Su Tafi Kurkuku a Abuja

"Dole mu bi doka da yin aiki tukuru wurin zamo wa abin koyi ga na baya, dole mu kasance babu wata kazanta a tare da mu."

A cikin sanarwar dankakin hukumar, Dele Oyewale ya fitar ya shawarci 'yan kasar da su ba su hadin kai wurin yaki da cin hanci.

"Ka cire sunana a misalinka", Akpabio ga Shugaban EFCC

A wani labarin, shugaban majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya gargadi shugaban hukumar EFCC da ya cire sunansa a misalin da ya ke na yaki da cin hanci.

Akpabio ya bayyana haka ne yayin da ake tantance Ola Olukoyede a majalisar a matsayin shugaban EFCC.

Wanna na zuwa ne bayan Ola ya yi misali da sunan Akpabio yayin da ya ke bayyana yadda za su yaki cin hanci a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.