Dakarun Sojoji Sun Murkushe Yan Ta'adda Masu Yawa a Sokoto
- Dakarun sojojin Najeriya masu aikin wanzar da zaman lafiya a jihar Sokoto sun smau nasarar halaka ƴan ta'adda masu ɗumbin yawa
- Dakarun sojojin sun samu wannan nasarar ne bayan sun kai wani samame a maɓoyar ƴan ta'addan da ke ƙauyen Tukandu na jihar
- Bayan sheƙe ƴan ta'addan masu yawa, dakarun sojojin sun kuma ƙwato makamai masu tarin yawa tare da babura guda tara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Jihar Sokoto - Dakarun sojoji na runduna ta takwas, a ranar Talata, 24 ga watan Oktoba sun kashe ƴan ta’adda da dama tare da ƙwato makamai a jihar Sokoto.
Hakan dai na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan hulɗa da jama'a na rundunar, Birgediya-Janar Onyema Nwachukwu, ya fitar.
Onyema ya bayyana cewa sojojin sun ƙaddamar da wani samame a tsanake a ƙauyen Tukandu, inda suka auka wa gungun ƴan ta’addan da suka yi kaurin suna, wadanda ke aikata munanan ayyuka a yankin baki ɗaya.
Tsshin Hankali Yayin da Jami'an Tsaro Suka Yi Artabu da Kasurgumin Dan Ta'adda a Babban Birnin Jihar Arewa
Ƴan ta'aɗda nawa sojojin suka halaka?
Ya ce munanan hare-haren da sojoji suka kai ya yi sanadiyar mutuwar ƴan ta'adda da dama, yayin da wasu suka arce da raunukan harbin bindiga.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A yayin da sojojin suka cigaba da kakkaɓe wajen bayan artabu da ƴan ta'addan, sun ƙwato bindigu kirar AK-47 guda uku, bindiga ƙirar PKT guda ɗaya, harsasai guda 125 masu kaurin 7.62mm, makamin roka guda biyu da babura tara.
Babban hafsan sojin ƙasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, ya yabawa sojojin tare da umartar su da su jajirce tare da cigaba da zafafa kai hare-hare kan ƴan ta’addan domin murƙushe su tare da hana su gudanar da ta'addanci.
Jihar Sokoto dai na daga cikin jihohin yankin Arewa maso Yamma da suke fama da matsalar rashin tsaro, wacce ta ƙi ci ta ƙi cinyewa.
Jami'an Tsaro Sun Fafata da Dan Ta'adda
A wani labarin kuma, jami'an tsaro sun yi artabu da wani ƙasurgumin ɗan ta'adda a cikin birnin Minna, babban birnin jihar Neja.
Jami'an tsaron waɗanda suka ɗauki lokaci suna artabun, sun ƙwato tarin makamai a gidan ɗan ta'addan tare da cafke matarsa da ƴaƴansa bayan ya tsere.
Asali: Legit.ng