Ba a Shirya Ba: ‘Dan Majalisa Ya yi wa CBN Kaca-Kaca Kan Tsadar Dala a Kasuwa
- Hon. Philip Agbese ya yi Allah-wadai da rikon da sabon Gwamnan bankin CBN ya ke yi wa tattalin arzikin kasa
- ‘Dan majalisar ya na ganin Dr. Yemi Cardoso ya kama hanyar da Godwin Emefiele ya bi yayin da yake bankin CBN
- Mataimakin kakakin ‘yan majalisar tarayyar ya na ganin babu hikima a cire takunkumin shigo da kayan waje
Abuja - Mataimakin mai magana da yawun bakin majalisar wakilai, Philip Agbese ya ce shugabannin bankin CBN ba su shirya da kyau ba.
Daily Trust ta rahoto Hon. Philip Agbese ya na kokawa cewa Dr. Yemi Cardoso da mataimakansa sun maimaita kuskuren Godwin Emefiele.
Kakakin majalisar ya ce kuskuren Mista Emefiele a CBN ya durkusa tattalin arzikin kasa.
An saida $1 a kan N1,200 a BDC
‘Dan majalisar ya yi wannan bayani ne bayan tsohon Ministan harkokin gona, Cif Audu Ogbeh ya kai masa ziyara a ofishinsa da ke Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana da labari an saida $1 a kan N1,200 a kasuwar canji (BDC), ana zargin tsarin da CBN ya fito da shi na karya darajar Naira ne ya jawo haka.
Hon. Agbese ya ke cewa tashin Dalar da aka samu ya nuna sababbin gwamnonin bankin CBN ya jawowa Najeriya ci-baya a maimakon a cigaba.
'Dan majalisa ya soki Yemi Cardoso
“CBN a karkashin jagorancin Cardoso ba ta shiryawa aikin ba. Duk da ya yi wuri, amma matakan da aka dauka sun nuna rashin kwarewa.
Sabon tashin kudin waje na Dala ya nuna cewa shugabannin CBN ba su fara da kyau ba."
- Philip Agbese
Cire takunkumi da (babban bankin CBN) aka yi ya jawo sukurkucewar Naira. Takunkumin nan ya taimaka wajen rike darajar Naira a baya.
Sahara Repoters rahoto ‘Dan majalisar ya na cewa yayi tunanin CBN zai kara yawan kayan da ba a bada kudi a shigo da su saboda a karya Dala.
"Kyau Tinubu ya binciki Buhari"
Jim kadan bayan lashe zaben 'dan majalisar tarayya, sai aka rahoto Philip Agbese yana cewa zai so a binciki gwamnatin Muhammadu Buhari.
Agbese ya ce garajen da ake yi wajen nade-nade daf da Bola Tinubu zai karbi mulki a karshen watan Mayun 2023 ya nuna da walakin a lamarin.
Asali: Legit.ng