Yan Bindiga Sun Kai Hari Wani Masallaci a Jihar Kaduna, Sun Kashe Limami

Yan Bindiga Sun Kai Hari Wani Masallaci a Jihar Kaduna, Sun Kashe Limami

  • Yan bindiga sun kai hari Masallaci lokacin sallar asuba a ƙauyen Sabon Layi, ƙaramar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna
  • Bayanai sun nuna cewa maharan sun kashe limamin Masallacin tare da wani mutum ɗaya yayin da wasu masallata biyu suka ji raunuka
  • Har yanzun babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnatin jihar Kaduna ko hukumar 'yan sanda

Jihar Kaduna - Wasu miyagun ƴan bindiga sun kai hari Masallaci a ƙauyen Sabon Layi da ke yankin ƙaramar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna lokacin Sallar Asuba yau Talata.

Ƴan ta'addan sun kashe limamin Masallacin da wani mutum ɗaya mai suna Kabiru, yayin da wasu ƙarin masallata biyu suka ji raunuka daban-daban.

Yan bindiga sun kashe limami lokacin sallar asuba a Kaduna.
Yan Bindiga Sun Kai Hari Wani Masallaci a Jihar Kaduna, Sun Kashe Limami Hoto: Punchng
Asali: UGC

Bilya Mairabo da Ashiru Mairabo, su ne suka ji raunuka yayin harin kuma yanzu haka suna kwance a babban Asibitin Jibrin Maigwari a Birnin Gwari ana musu magani.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kashe Jami'in Tsaro, Sun Buɗe Wa Motocin Matafiya Wuta a Arewa

Wani Basarake a yankin, Zubair AbduRrauf, ya shaida wa Punch ta wayar tarho cewa lamarin ya faru ne a lokacin sallar asuba da misalin karfe 5 na safe, Vanguard ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Harin 'yan bindiga ya zama ruwan dare a Birnin Gwari

AbduRrauf, wanda ke rike da sarautar Danmasanin Birnin-Gwari, ya ce kusan kullum ‘yan bindiga sai sun kai hari a kauyukan Birnin-Gwari.

A cewarsa, suna kashe rayukan al'umma, su yi garkuwa da wasu domin neman kuɗin fansa, musamman ma manoma.

Ya kara da cewa lamarin ya fi muni a babban titin Birnin-Gwari zuwa Kaduna, wanda a yanzu ya zama ruwan dare ga matafiya da sauran masu amfani da hanyar.

A kalamansa ya ce:

"Eh, an kashe limamin masallaci da wasu masallata biyu. Lamarin ya faru ne da misalin karfe 5 na safiyar ranar Talata. Wasu masallata biyu suna babban asibitin Jibrin Mai Gwari, Birnin-Gwari ana musu magani."

Kara karanta wannan

Rayuka da Dama Sun Salwanta a Wani Mummunan Hatsarin Mota da Ya Auku a Kan Babban Titi a Najeriya

"Muna cikin wani mawuyacin hali a Birnin-Gwari. Ko a kan babban titin Kaduna zuwa Birnin Gwari, mutane ba su iya wucewa sai da rakiyar jami’an tsaro ko ‘yan banga."
"Kwanaki biyu da suka gabata ‘yan bindiga sun kashe mutane biyu da suke dawowa daga Kaduna. Suna kawo hari kusan kowace rana. Jami'an tsaro na iya bakin kokarinsu amma akwai bukatar canja dabaru."

Hukumomi sun san abin da ya faru?

Kawo yanzu dai babu wani sanarwa a hukumance daga gwamnatin jihar Kaduna ko kuma rundunar ‘yan sandan har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Mansir Hassan, ya bayyana cewa yana wani abu ne, ba zai iya magana ba a yanzu.

Jikar Ɗantata ta kwanta dama

A wani rahoton na daban Allah ya yi wa Batulu Alhassan Baba Ahmad Dantata rasuwa tan ada shekaru 40 a duniya.

Marigayya jika ce ga fitaccen attajirin nan, Alhaji Aminu Ɗantata, kuma ta rasu ne bayan fama da cutar sikila a asibitin ƙasar Saudiyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262