Majalisar Jihar Benue Ta Bai Wa Gwamna Alias Wa’adin Awanni 72 Don Nada Hadimi a Bangaren Tsaro

Majalisar Jihar Benue Ta Bai Wa Gwamna Alias Wa’adin Awanni 72 Don Nada Hadimi a Bangaren Tsaro

  • Yayin da rashin tsaro ke kara kamari a Arewa ta Tsakiya, majalisar jihar Benue ta bai wa gwamnan jihar wa’adin kawo gyara a harkar tsaro
  • Majalisar ta ba da wa’adin awanni 72 ga Gwamna Alias Hyacinth don nada hadiminsa a bangaren tsaro don samun sauki a jihar
  • Wannan na zuwa ne bayan wasu gungun ‘yan fashi sun kai farmaki kan wasu bankuna a Otukpo tare da ajalin jami’an tsaro

Jihar Benue – Majalisar dokokin jihar Benue ta bai wa Gwamna Hyacinth Alias wa’adin kwanaki uku da ya yi gaggawar nada hadimi a bangaren tsaro.

Majalisar ta ba da wannan wa’adin ne bayan mummunar fashin bankuna da ya afku a ranar Juma’a 20 ga watan Oktoba a Otukpo jihar Benue.

Majalisar jihar Benue ta bai wa gwamna wa'adin kwanaki uku don nada hadimi a harkar tsaro
Majalisa a Benur Ta Bai Wa Gwamnan Alias Wa’adin Awanni 72 Don Daukar Mataki. Hoto: Alias Hyacinh.
Asali: Facebook

Wane doka majalisar ta kafa kan rashin tsaro a Benue?

Kara karanta wannan

Da Dumi-dumi: Majalisa Ta Dauki Mataki Kan Gwamnan CBN Game da Cire Dokar Shigo da Kayayyaki 43

Majalisar ta ce wannan abin takaici da ya faru na da alaka da rashin tuntubar jami’an tsaro inda aka shafe awanni biyu ana fashin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan wa’adi na zuwa ne bayan kudirin da mamban majalisar mai wakiltar mazabar Otukpo/Akpa, Angbo Kennedy ya gabatar a gaban majalisar.

Kakakin majalisar, Aondona Dajoh yayin tabbatar da kudirin ya bai wa gwamnan jihar wa’adin kwanaki uku da ya nada hadiminsa ta fannin tsaro.

Meye majalisar ke kokawa kan rashin tsaro a Benue?

Daya daga cikin mambobin majalisar, Godwin Edoh ya bayyana yadda ya sha da kyar saboda fashin bankin da aka yi a Otukpo, cewar Channels TV.

Mamban ya ce ‘yan fashin sun yi amfani da abin fashewa yayin fashin inda ya bayyana halin da ya shiga saboda kawai babu wanda zai tuntuba musamman mai ba da shawara kan harkokin tsaro.

Kara karanta wannan

Nyesom Wike Ya Kinkimo Doka, Marasa Biyan Haraji Za Su Tafi Kurkuku a Abuja

Ya ce kokarin sanar da shugabannin kananan hukumomi ya ci tura saboda dukkansu an dakatar da su na tsawon lokaci tun watan Yunin 2023, Naija Times ta tattaro.

‘Yan sanda sun cafke mutane 4 kan zargin fashi a Benue

A wani labarin, jami’an tsaro sun cafke wasu matasa hudu kan zargin fashi da makami a Otukpo da ke jihar Benue.

A ranar Juma’a 20 ga watan Oktoba ne wasu gungun ‘yan fashi su ka kai farmaki kan wasu bankuna a jihar wanda hakan ya yi sanadin rasa rayuka.

‘Yan sanda sun sanar da cewa harin ya yi sanadin mutuwar DPO da wasu jami’ansu guda uku a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.