Kotun Amurka Ta Hana FBI Da CIA Fitar Da Bayanan da Za Su Iya Tona 'Asirin' Tinubu
- Kotun mazabar Columbia a Amurka ba ta yarda a tursasawa jami’an gwamnati fitar da bayanai game da Bola Ahmed Tinubu ba
- Alkalin da ya saurari karar a makon nan, ya ce lauyoyin Aaron Greenspan ba su iya gamsar da shi muhimman sakin bayanan ba
- Aaron Greenspan ya na so ya samu bayanai kan shari’ar da aka yi a kan harkar kwayoyi da shugaban Najeriya a kasar Amurka
United States - Wata kotun mazaba da ke Columbia ta ki amincewa da bukatar Aaron Greenspan na neman bayanai kan Bola Ahmed Tinubu.
Mista Aaron Greenspan ya shigar da kara ya na mai neman kotun ta tursasawa jami’an tsaro fitar bayanan da su ka shafi shugaba kasar Najeriya.
The Nation ta ce a hukuncin da Mai shari’a Beryl A. Howell ya zartar a ranar Litinin, ya ki amincewa da bukatar gaggawan da aka gabatar masa.
Tinubu: An yi karar FBI, EOUSA, CIA a kotu
Idan da Greenspan ya yi nasara, hukuncin zai shafi EOUSA, sakataren gwamnatin Amurka, FBI, hukumar tattara haraji na kasar Amurkan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sauran wadanda aka hada a karar sun hada da hukumar kula da harkar kwayoyi da CIA.
Abin da mai shigar da kara ya nema shi ne a fitar da bayanan da ya nuna za a bukace su a shari’ar zaben Najeriya da ake yi yanzu a kotun koli.
A bayanin da ya gabatar a kotun da ke Columbia, Greenspan ya shaida cewa da gan-gan kotun koli ta fara sauraron karar zaben shugaban kasa.
Baya ga Mai girma Bola Tinubu, ana neman bayanai kan Mueez a shari’ar mai lamba 23-1816.
Kotu ta kare sirrin Bola Tinubu
Sahara Reporters ta ce abin da kotun ta duba shi ne mai karar bai iya gamsar da ita dalilin watsi da sirrin Tinubu wajen saki bayanansa a fili ba.
Kotun ta bukaci a nuna mata hujjar da za ta jawo a jinginar da suturar da doka ta ba shugaban Najeriyan saboda abin da zai amfani sauran jama’a.
Bola Tinubu ya kai kara a kotu
Ana da labarin yadda Bola Tinubu ya ke yin bakin kokarinsa domin a hana fitar da bayanan shari'ar da aka yi da shi a wata kotun Amurka a 1993.
Ku na da labari Aaron Greenspan ya dogara ne da dokar FOI wajen samun bayanan.
Asali: Legit.ng