Jami'an Tsaro Sun Kashe Dan Bindiga, Sun Ceto Mutane a Jihar Kebbi

Jami'an Tsaro Sun Kashe Dan Bindiga, Sun Ceto Mutane a Jihar Kebbi

  • 'Yan bindiga sun kwashi kashinsu a hannu yayin da jami'an tsaro suka haɗu suka kai musu samame har cikin daji a jihar Kebbi
  • Gwarazan dakarun da suka haɗa da sojoji, yan sanda, DSS da Sibil difens sun ceto mutane uku da aka sace, sun sheƙe ɗan bindiga
  • Gwamna Nasiru Idris Kauran Gwandu ya bada umarnin tura ƙarin jami'an tsaro domin dakile hare-hare a wasu ƙananan hukumomi

Jihar Kebbi - Jami'an tsaron haɗin guiwa da suka ƙunshi, dakarun sojoji, yan sanda, DSS da jami'an Sibil Difens sun ragargaji 'yan bindiga a jihar Kebbi ranar Lahadi.

A rahoton da Jaridar Daily Trust ta tattaro, ya nuna cewa gwarazan jami'an tsaron sun ceto mutane uku da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a dajin Kanzanna da ke ƙaramar hukumar Bunza.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Wasu Tsageru Sun Shiga Har Ɗakin Kwana, Sun Kashe Ɗaliba a Jihar Arewa

Gwamnan jihar Kebbi, Nasiru Idris.
Jami'an Tsaro Sun Kashe Dan Bindiga, Sun Ceto Mutane a Jihar Kebbi Hoto: Nasiru Idris
Asali: UGC

Jami'an tsaron haɗin guiwar sun kuma aika wani hatsabibin ɗan bindiga zuwa lahira yayin da wasu da dama suka gudu ɗauke da raunukan harbin bindiga.

Wannan nasara ta samu ne biyo bayan samamen da dakarun sojojin Najeriya suka kai kan ƴan bindigan, waɗanda suka hana al'umma zaman lafiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gabanin wannan samame, 'yan bindigan jejin sun kai hare-hare masu yawa kan fararen hula a kananan hukumomin Kalgo, Bunza da kuma Arewa, PM News ta ruwaito.

Wane mataki gwamnati ta ɗauka?

Daraktan tsaro na ofishin majalisar zartarwa na Birnin Kebbi, AbdulRahman Usman, ya ce Gwamna Nasiru Idris ya bada umarnin tura karin jami’an tsaro.

Ya ce mai girma gwamna ya bada umarnin hanzarta tura ƙarin dakarun tsaro zuwa ƙananan hukumomin da lamarin 'yan bindiga ya taɓa domin tsare rayuka da dukiyoyin jama'a.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kashe Jami'in Tsaro, Sun Buɗe Wa Motocin Matafiya Wuta a Arewa

"Ya kuma ba da umarnin samar da isassun tallafin kayan aiki ga jami'an tsaro na hadin gwiwa domin ƙara inganta ayyukansu." in ji shi.

Jihar Kebbi na ɗaya daga cikin jihohin Arewa maso Yamma da ke fama da hare-haren ta'addancin 'yan bindiga da garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.

Wani Jirgi Ya Yi Hatsari Bayan Mai Ya Kare

A wani rahoton kuma Ana fargabar mutane da dama sun mutu yayin da wani jirgin ruwa ya yi hatsari a ƙaramar hukumar Ovia ta Kudu maso Yamma a jihar Edo.

Hukumar 'yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin ranar Litinin inda ta ce mutum ɗaya ne ya mutu a hatsarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262