Mutum Daya Ya Mutu Yayin da Jirgin Ruwa Ya Yi Hatsari a Jihar Edo

Mutum Daya Ya Mutu Yayin da Jirgin Ruwa Ya Yi Hatsari a Jihar Edo

  • Ana fargabar mutane da dama sun mutu yayin da wani jirgin ruwa ya yi hatsari a ƙaramar hukumar Ovia ta Kudu maso Yamma a jihar Edo
  • Hukumar 'yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin ranar Litinin inda ta ce mutum ɗaya ne ya mutu a hatsarin
  • Sai dai shugaban karamar hukumar, Blessing Perewari, ya ce wasu sun tsira da rayuwarsu amma mutum 7 ne suka mutu

Jihar Edo - Hukumar 'yan sanda reshen jihar Edo ta bayyana cewa mutum ɗaya ya mutu yayin da wasu huɗu suka jikkata a hatsarin jirgin ruwan da ya auku a Gelegele, ƙaramar hukumar Ovia.

Jaridar Punch ta tattaro cewa hatsarin ya afku ne yayin da jirgin ruwan na haya ya bugi wani jirgin ruwa da ke tsaye a bakin gaɓa ranar Alhamis da ta gabata.

Kara karanta wannan

Mutane 2 Sun Mutu Yayin da Wasu 10 Su Ka Jikkata Bayan Bishiya Ta Fado Kansu a Jihar Arewa

Jirgin ruwa ya yi haɗari a jihar Edo.
Jirgin Ruwa ya gamu da hatsari a jihar Edo Hoto: punchng

Sai dai mazauna yankin sun koka kan cewa akalla mutane 7 ne suka mutu sanadin hatsarin da ya faru a jihar Edo.

Jirgin ruwan ya kwaso galibi mata da kananan yara an ce man fetur ne ya kare masa bayan da wani fasinja ya sauka a daya daga ƙauyukan da ke kan hanya a Kogin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An bayyana cewa tun farko jirgin ruwan ne ya sauka daga asalin hanyar da ya kamata ya bi, bayan haka ne ya ci karo da wani jirgin na daban.

Yan sanda sun tabbatar

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Chidi Nwabuzor, ya tabbatar da faruwar hatsarin, inda ya ce mutum daya ne ya mutu.

A kalamansa ya ce:

"'Yan sandan ruwa sun tabbatar da cewa mutum ɗaya ne ya rasa rayuwarsa, wasu huɗu kuma suka jikkata yayin da aka samu nasarar ceto sauran cikin ƙoshin lafiya."

Kara karanta wannan

Yanzun nan: Tsageru sun yi yunkurin kashe gwamnan APC a Arewa, bayanai sun fito

Mutum 7 suka mutu

Shugaban ƙaramar hukumar, Blessing Perewari, wanda ya kai ziyara wurin da haɗarin ya auku, ya kuma jajantawa iyalan waɗan da lamarin ya shafa.

Ya ce tuni aka ɗauki gawar mutanen da suka mutu zuwa ɗakin ajiyar gawarwaki, kamar yadda Tribune Online ta ruwaito.

Ya ce:

"Tare da taimakon 'yan sandan ruwa da sauran al'umma, mun sami damar ceto 18 daga cikin fasinjojin yayin da bakwai suka mutu."

Yan Bindiga Sun Halaka Mafarauci da Direbobi Biyu a Kaduna

A wani rahoton kuma Tsagerun 'yan bindiga sun halaka jami'in tsaro mafarauci da wasu direbobi biyu a titin Birnin Gwari da ke jihar Kaduna.

Wani mazaunin garin ya bayyana cewa kusan kullum sai an yinjana'iza ta waɗan da suka ɓata a yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262