Fetur ya Haura N680 a Gidajen Mai, Farashin Gas da Dala Duk Sun Lula a Kasuwa
- Man fetur ya na cigaba da kara tsada a Najeriya duk da kamfanin NNPCL ya musanta zargin cewa mai ya soma yin karanci
- Daga N620 da gwamnatin tarayya ta yanke a kwanakin baya, wasu ‘yan kasuwan sun harba farashinsu har ya kusa kai N700
- A jihohin Arewa da su ka fi nisa da manyan tashoshin mai, akwai gidajen da litar mai ta kai N680 bayan gas da ya tashi sosai
Abuja - A wasu gidajen mai da ke musamman Arewacin kasar nan, farashin man fetur gaba-gaba kurum yake yi a kowace rana.
A farkon makon nan, rahoton Punch ya tabbatar da cewa akwai wasu gidajen man da ake saida litar fetur kan N685 a halin yanzu.
Farashin da ‘yan kasuwan su ke saida mai ya zarce abin da gwamnati ta kayyade masu, ana tunanin kudin man zai iya kai N720.
Man fetur ya tashi sau 2 a wata 2
A Yuli ne NNPCL ya kara kudin lita daga tsakanin N537 da N550 zuwa N617 a jihohin Arewa, sakamakon canjin kudin danyen mai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta jawo mutanen jihohin kudancin Najeriya su na sayen fetur a kan N580 zuwa N600, farashi ya danganta da nisan dako.
Ana tsadar fetur a jihohin Arewa
Duk da karin farashin da aka samu a yau, rahoton ya ce akwai karancin man fetur a irinsu Sokoto, kuma lita ta kai N680 zuwa N685.
Yayin da ake saida kowane litar fetur din a kan N615-N620 a gidajen man NNPCL, ‘yan kasuwa sun harba farashinsu a garuruwa.
Legit.ng Hausa ta lura manyan gidajen mai irin A. A Rano da Matrix ne su ke saida man su a kan N620 zuwa N650 a Zariya da Kaduna.
An Gudu Ba a Tsira Ba: 'Yadda Matatar Man Dangote Za Ta Jawo Tsadar Mai da Wasu Sauye-sauye a 2024', Rahoto
A safiyar Talata, wani ma'aikaci ya shaida mana ya saye litar fetur a kan N640, mu na da labari tun a kwanakin baya farashin ya kai N630.
...kilon gas ya na kara tsada
A wasu gidajen man, farashin ya zarce haka baya ga kukan cewa litarsu ba ta da kyau, idan an yi sa’ar samun man kenan a garuruwan.
Wani mazaunin Kaduna ya fada mana litar fetur ta kai N650 sannan sai mutum ya lale N12, 000 zai cika tulun gas mai cin kilogiram 12.5.
A cewar wani da ya saye gas a tashar A.A Rano a Zariya, an saida masa kilo a N900.
Za a tsaida tashin Dalar Amurka
A makon nan aka zo da labari cewa Gwamnatin Bola Tinubu na kokarin hana Dala cigaba da tashin kullum-yaumin a kasuwar canji.
Ministan tattalin arzikin Najeriya, Wale Edun ya sanar da cewa akwai $10bn na kudin kasar waje da za a samu nan da makonni kadan.
Asali: Legit.ng