Igboho Ya Bai Wa Makiyaya Wa’adin Kwanaki 7 Su Bace Daga Yankin Yarbawa

Igboho Ya Bai Wa Makiyaya Wa’adin Kwanaki 7 Su Bace Daga Yankin Yarbawa

  • Kwanaki kadan bayan samun ‘yanci, Sunday Igboho ya bai wa Fulani makiyaya wa’adin kwanaki bakwai da su bar yankin
  • Igboho wanda ke fafutukar kafa kasar Yarbawa ya yi wannan gargadi ne ganin yadda ake kashe jama’a a yankin
  • Ya ce ba za su lamunci yadda makiyaya ke kashe manoma a yankunansu ba da kuma hana su yin noma

Jihar Oyo - Mai fafutukar kafa kasar Yarbawa, Sunday Adeyemo Igboho ya umarci dukkan Fulani ma su kiwo su bace daga yankin Kudu maso Yammacin kasar.

Igboho ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa a jiya Lahadi 22 ga watan Okotoba inda ya bai wani makiyayan kwanaki bakwai kacal, Legit ta tattaro.

Igboho ya bai wa makiyaya wa'adin kwanaki bakwai su bar kasar Yarbawa
Igboho ya gargadi makiyaya su bar yankin Yarbawa. Hoto: Sunday Igboho.
Asali: Facebook

Wane gargadi Igboho ya bai wa makiyaya?

Ya ce ya dauki wannan matakin ne ganin yadda makiyayan ke kashe manoma a jihohin Oyo da Ogun.

Kara karanta wannan

Tattalin Arziki: Abin Da Cire Takunkumin CBN Yake Nufi Ga Manoma Da Abinci, Masani

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bukaci jami’an tsaro da su zakulo makiyayan da ake zargi da kisan manoma a yankin Iwele-Ile da ke jihar Oyo da kuma wasu yankuna a jihar Ogun.

Mai fafautukar ya kara da cewa yankin Yarbawa da ma sauran yankunan kasar na bukatar zaman lafiya ganin yadda makiyayan ke hana su aiki a gonakinsu.

Sanarwar ta ce:

“Mu na kira ga jami’an ‘yan sanda da farin kaya da hukumar NSCDC da sojoji da su kawo karshen wannan matsalar kafin ya wuce gona da iri.
“Irin kwanton bauna da su ka yi wa jami’an Amotekun wadanda ke kokarin kare lafiyar mu ya kamata a dauki mummunan mataki a kansu.”

Wane kira Igboho ya yi wa Tinubu kan makiyaya?

Sunday ya yabawa gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde da na Ogun, Dapo Abiodun kan kokarinsu na kawo zaman lafiya a jihohinsu, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Bashin Karatu: Kamata Ya Yi Dalibai Su Yi Zanga-Zangar Kin Amincewa Da Tsarin, In Ji Mai Fashin Baki

Ya kara da cewa:

“Mu na bai wa makiyaya wa’adin kwanaki bakwai da su tattara su bar wannan yankin Yarbawa, wannan gargadi ya na da matukar tasiri.
“Ba za mu dauki mataki da hannunmu ba amma dole ne su bar wannan yanki na mu.”

A karshe, ya bukaci Shugaba Tinubu da ya yi kokarin kare rayukan mutane da dukiyoyinsu a kasar.

Igboho ya shaki iskar ‘yanci bayan shekaru 2 a kulle

Kun ji cewa, mai fafutukar kafa kasar Yarbawa, Sunday Igboho ya shaki iskar ‘yanci bayan shafe shekaru biyu a kulle.

Igboho bayan fitowarshi ya godewa tsohon shugaban kasa, Obasanjo da wasu dattawan Yarbawa da kokarinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.